Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari ya tabbatar da nadin Mohammed Adamu a matsayin IGP na ‘Yan Sanda

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Alhamis da ta gabata, Majalisar Dinkin Duniya a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sanya da tabbatar da Mohammed Adamu a matsayin Babban Jami’in Tsaro na ‘yan sandan Najeriya.

Ka tuna a baya, ranar 15 ga watan Janairu 2019, shugabancin kasar a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta nada Mohammed a matsayin mai wakilcin Jami’an tsaron Najeriya (IGP), don maye gurbin tsohon IGP, Ibrahim Idris.

Shugaba Buhari ya gabatar da Adamu ne da maye gurbin Mista Idris, tsohon shugaban Jami’an tsaron, a ganin cewa lokacin da zai yi ritaya ya gabato.

Ko da shike kamin hakan, al’ummar Najeriya a lokacin na zargin cewa shugaba Buhari bai son ya dakatar da Idris duk da cewa ya kai ga shekarun ritaya daga aikin tsaron kasar.

Sabon Jami’in da aka tabbatar da nadin shi a jiya, IGP Mohammed Adamu mutumin Lafia ne, babban birnin tarayyar Jihar Nasarawa, ya kuma karanci Geography a babban makarantar Jami’a.

Adamu ya shiga aikin Dan Sanda ne tun ranar 1 ga watan Fabrairun 1986, a matsayin CASP.

Ya kuma yi zaman Kwamishanan Tsaro a Jihar Ekiti, Enugu da kuma zaman Mataimakin Insfekta Janar na ‘Yan Sandan Zone 5, a Hedikwatar da ke a Benin, Jihar Edo.

KARANTA WANNAN KUMA; Ka bani karin Wata Uku da gyara Jihar Nasarawa, Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya roki Gwamna Abdullahi