Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Salisu Mu’azu da wasu mutane biyu sun samu Yanci daga ‘yan Mahara

Published

on

at

advertisement

Shahararran Mai Hadin Fim a Kannywood, Salisu Muazu, tare da wasu mutane biyu sun samu yancin ransu daga hannun ‘yan hari da makami bayan rana biyu da aka sace su a babban hanyar da ta bi Kaduna zuwa Jos, a ranar Alhamis da ta gabata.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bisa bayanin da dan uwan Salisu, Alhaji Sani Muazu ya bayar ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadin da ta wuce a birnin Kano, cewa lallai Mahara da Bindigar sun saki dan uwansa Salisu Mu’azu.

Sani ya bayyana da cewa ‘yan harin sun saki su ukun ne bayan da suka biya kudin yanci na naira Miliyan Goma (N10m), kamar yadda aka bukace su da biya.

“Mun biya su Miliyan Goma, suka kuma tura mu a wani wuri daban da inda ‘yan uwanmu suke. A yayin da muke cikin rudu, wani direban babban mota da ya biyo hanyar da ya kuma gana da su ya gwada mana inda suke, muka kuma gana da su” inji Sani.

Bisa bayanin manema labarai, an bayyana cewa an sace Salisu ne da sauran mutane biyun a yayin da suke kan dawo wa a Jos daga wata taro da suka tafi a Jihar Kaduna, anan ne Mahara da Bindiga suka tare su, suka kuma sace mutum uku daga cikin su.

Ko da shike su hudu ne ke a cikin motar kamin aka tare su, amma shi Sani ya samu tserewa da barin kanin sa Salisu da sauran mutane biyun.

Sani da Salisu dan uwansa shahararru ne a shafin hadin fim a Kannywood tun da dadewa.

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli yada wani ya biya wa kansa kudin makarantan Babban Jami’a har ya kamala da Turin Baro.