Labaran Najeriya
Ka Manta da zancen Gina wa Fulani Gidan Radiyo, Urhobo sun Kalubanlanci Buhari
Hadaddiyar Kungiyar ‘yan Urhobo (UPU) sun gargadi Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da manta da zancen ginawa Fulani wata gidan Radiyo.
UPU wata Kungiyar ‘yan yaran Urhobo ne daga Jihar Benue, satsan kuducin kasar Najeriya.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa ‘yan kungiyar sun gabatar da gargadin ne ga Buhari daga bakin Shugaban su na tarayya, Olorogun Moses Taiga.
“Ka manta da duk wata shiri da zancen gina wa al’ummar fulani gidan radiyo, hakan bai dace ba a wannan lokaci da kasar ta ke a ciki” inji Taiga.
Taiga ya shawarci gwamnatin Najeriya da kafa kai ga kadamar da ayukan da zasu taimaka wa ci gaban tarayyar al’ummar kasar Najeriya.
A bayanin Taiga “Kungiyar UPU na murna da kuma fahariya da duk wata kadamarwa na rabar da rahotannai a yaruka da dama a kasar. Amma gina wa Fulani gidan Radiyo a wannan lokaci da kasar ke a cike, bai dace ba” inji shi.
Naija News Hausa ta gane da cewa tun lokacin da shugaba Buhari ya gabatar da wannan shirin, da yawa cikin alummar Najeriya sun bayyana rashin amincewa da shirin.
Ka tuna da cewa shugaba Muhammadu Buhari bafulace ne, daga Daura, Jihar Katsina.