Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 5 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 5 ga Watan Yuni, 2019

1. An gane da kudin cin hanci £211m da ke da liki da Abacha

Wata bankin kasar Turai, Jersey ta gane da wata kudin cin hanci da rashawa na kudin Euros miliyan £211,000,000 (N81.9bn) da ke da liki da tsohon shugaban Najeriyar, Janar Sani Abacha, a mulkin sojoji.

Bisa wata rahoto da aka bayar a kasar UK ga Naija News, ta bayyana da cewa an sanya kudin ne a wata asusun ajiyar kudi da ke a Jersey a wakilcin wata kamfanin Turai ta Doraville Properties Corporation.

2. An sanya Muhammad-Bande a matsayin shugaban hukumar UNGA

An nada dan Najeriya, Ambasada Tijjani Muhammad-Bande a matsayin shugaban tarayyar Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) na 74 a tarihi.

Naija News ta fahimta da cewa an nada Tijjani ne ga shugabancin a ranar Talata, 4 ga watan Yuni da ta gabata a birnin New York.

3. Kungiyar Ma’aikata sun kafa baki ga zancen albashin ma’aikata na naira dubu 30,000

Kungiyar Ma’aikatan kasar Najeriya sun yi watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo da cewar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kasa ga cika arjejeniyar ta akan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu Talatin da aka gabatar a baya.

Shugaban kungiyar, Mista Bobboi Kaigama, a ranar Litini da ta gabata a birnin Akure, a wata gabatarwa da yayi, ya ce ”ba karya bace sabon tsarin kankanin albashin ma’aikata da shugabancin Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta gabatar ba” inji shi.

4. Titus Uba ya lashe kujerar kakakin majalisar wakilai ta Benue

Tsohon kakakin yada yawun gidan majalisar wakilai ta jihar Benue, Titus Uba da ke wakilcin yankin Kyan ya sake lashe tseren zaman kakakin majalisar a karo ta biyu.

Haka kazalika mataimakin sa, Christopher Adaji da ke wakilcin yankin Ohinmini shima ya ci zaben zama mataimaki.

5. Ku dakatar da Sanusi – inji Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Hukumar bincike da rashin amincewa da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano sun gabatar da goyon bayan cewa a tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi.

Naija News Hausa ta fahimta cewa kungiyar ta bukaci hakan ne bayan da aka gane sarkin da laifin makirci da cin hanci na naira biliyan N3.4b.

7. Sakon shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya a bayan sallar Eid-el-Fitr

A ranar Talata da ta wuce, an gano da shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake addu’a hade da wasu a masalacin idi da ke a barikin Mabilla, anan birnin tarayya, Abuja.

A bayan hakan ne shugaba Buhari ya gargadi Musulumai da ci gaba da hali ta gari bayan wucewar azumin Ramadani da aka kamala.

8. ‘Yan Kwallon Kafa ta Najeriya sun ki dawowa bayan wasar su da kasar Senegal

Kungiyar ‘yan kwallon kafa ta Najeriya ‘Flying Eagles’ ta kaurace da barin gidan kwanar su a birnin Poland, bayan wasar su da Senal.

Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan kwallon sun ki dawowa ne da zargin cewa anki biyan su kudin wasan da suka buga a ranar Litini da ta wuce.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com