Connect with us

Uncategorized

Sojojin Najeriya sun harbe Mutane 2 a wata Zanga-Zanga a Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An harbe mutane biyu a wata farmaki da ya tashi a yayin da tulin mutane ke wata zanga-zanga a shiyar Gurin, a karamar hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.

Naija News Hausa ta gane da cewa mutanen yankin sun fita zanga-zangar ne akan rashin amincewa da hana amfani da babura da aka gabatar a Jihar.

Da safiyar ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni 2019, mazaunan shiyar Gurin sun mamaye garin da zanga-zanga don bayyana rashin amincewarsu da dokar da Jami’an tsaro suka bayar na cewa kada kowa ya kara fita ko amfani da babur a Jihar.

Jami’an tsaron da hadin kan gwamnatin Jihar ta bada umarnin dakatar da amfani da babur ne da zargin cewa ‘yan fashi, mahara da bindiga da ‘yan ta’addan Jihar na amfani da wannan damar don kai hari da satar mutane a yankunan Jihar.

A bayanin wani mazaunin kauyan Gurin da manema labarai da tsakar ranar Alhamis, ya bayyana da cewa mutum biyu daga cikin mutane shidda da Sojoji suka harbe sun mutu.

“Lallai gaskiya ne, mutane biyu sun mutu a harbin da Sojoji suka yi, Mazauna kuma sun fita zanga-zangar ne don ba wata dalili ko muhinmancin ta gaske da ya kai ga hana amfani da babur a yankin” inji shi.

“Da yawar mazaunan Gurin manoma ne duka, kuma suna bukatar baburar su don shiga daji da kadamar da ayukan su kamar yadda suka saba, don wannan ne kawai abin tafiya a gare su.”

Naija News Hausa ta gane bisa rahotannai da ake karba daga Jihar Adamawa, cewa jihar na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda.