Connect with us

Uncategorized

Kalli dalilin da yasa Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarakai biyu a ranar guda

Published

on

Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar CIKA Ibrahim da wakilin kauyan Kanoma, Alhaji Ahmed Lawal da zargin hada hannun da ‘yan ta’adda a Jihar.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa wata sanarwa da aka bayar daga hannun Alhaji Yusuf Idris, darakta Janar na sadarwa ga Gwamnan Jihar, a jagorancin sabon gwamnan Jihar, Alhaji Bello Matawalle.

Gwamnatin Jihar ta tsige ‘yan sarauta biyun ne bayan zarge-zarge da alamar da aka gane da su na hada kai da ‘yan hari don aiwatar da mumunar hali a yankin.

A haka kuma aka bukacesu da barin kujerar wakilcin su da kumar mikar da gurbin ga wasu har sai an gama bincike kan zargin.

A fahimta da ganewar Naija News Hausa, bisa rahotannai da tarihi kuma, a karamar hukumar Maru inda aka tsige masu sarauta biyun ne mahara da bindiga suka fara kai hari a kauyan Langido a shekarar 2011 da ta shige a baya.

Ka tuna da cewa a baya kuma, tsohon gwamnan Jiahr, Alhaji Abdul’aziz Yari da tsige ‘yan sarauta shidda a Jihar a lokacin da yake kan jagoranci.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa rundunar Sojojin Najeriya sun harbe mutane biyu a wata farmaki da ya tashi a yayin da tulin mutane ke wata zanga-zanga a shiyar Gurin, a karamar hukumar Fufore ta Jihar Adamawa.

Wannan ya faru ne a yayin da mutanen yankin sun fita zanga-zanga akan rashin amincewa da umarnin hana amfani da babura da jami’an tsaro a goyon bayan gwamnatin jihar ta gabatar da shi.