Uncategorized
Kalli Jerin Shugabanan Sanatoci da suka yi jagoranci a Najeriya tun shekarar 1960
Mun sanar a Naija News Hausa ‘yan sa’o’i da suka wuce da hidimar zaben sabon shugaban Gidan Majalisar Dattijai na 9.
Hidimar da aka yi a yau Talata, 11 ga watan Yuni 2019, ya karshe da murna ga Jam’iyyar APC, a yayin da dan takaran su a kujerar shugabancin gidan Majalisar, Ahmed Lawan da mataimakin sa, Ovie Omo-Agege suka lashe tseren zaben.
Hakan ya tabbata ne bayan da suka fiye ‘yan adawar su daga Jam’iyyar PDP da yawan kuri’u a zaben.
Tun daga shekarar 1960 da kasar Najeriya ta karbi yancin dayantakewa a shugabanci, kasar har ga wannan shekara ta karbi shugabancin shugabannai 14 a Majalisar Dattijai, daga Jam’iyu daban-daban.
Kalli jerin sunayan su a kasa da shekarun da suka yi jagoranci;
Sunan Shugabannan Sanatoci | Sa’a/Shekarar mulki | Jam’iya |
---|---|---|
Nnamdi Azikiwe | 1960 | NCNC |
Dennis Osadebay | 1960-1963 | NCNC |
Nwafor Orizu | 1963–1966 | NCNC |
Joseph Wayas | 1979–1983 | NPN |
Iyorchia Ayu | 1992–1993 | SDP |
Ameh Ebute | 1993 | SDP |
Evan Enwerem | 1999 | PDP |
Chuba Okadigbo | 1999–2000 | PDP |
Anyim Pius Anyim | 2000–2003 | PDP |
Adolphus Wabara | 2003–2005 | PDP |
Ken Nnamani | 2005–2007 | PDP |
David Mark | 2007-2015 | PDP |
Bukola Saraki | 2015-2019 | PDP |
Ahmed Ibrahim Lawan | 2019 – present | APC |
KARANTA WANNAN KUMA; Ba zamu bada Filin kiwo ba ga Fulani a Jihar mu – Kungiyar Iyamirai (Ohanaeze) sun yi barazanar haka.