Connect with us

Labaran Najeriya

Dimokradiyya: Abinda shugaba Buhari ya fada a zaman Liyafa da Manyan Shugabannan Kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ga bayanai da hotunan shugaba Buhari tare da Manyan shugabannai a zaman Liyafa kamin ranar Dimokradiyya

A daren ranar Talata da ta wuce, shugaba Muhammadu Buhari ya marabci manyan shugabannan kasashen waje a wata zaman liyafa da ya hada ‘yan sa’o’i kadan da hidimar sabon ranar Dimokradiyya, 12 ga watan Yuni.

Bisa binciken Naija News, zaman liyafar ta samu halartan gwamnonin kasar Najeriya, sabbin ‘yan Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai, Manyan Ma’aikata a kasar da kuma Manyan Masana’anta da masu zuba jari a kasar Nerjiya.

A yayin da ake cikin liyafar, shugaba Buhari ya kara tunar da al’umma da cewa gurin shugabancin sa itace ganin cewa sun kai kasar Najeriya gaba (Next Level).

”Zamu karfafar da zaman Lafiya, Kadamar da Adalci da kuma tabbatar da cin nasara a tattalin arziki ga ‘yan Najeriya duka” in ji shi.

Shugaba Buhari ya kara da yin bayyani game da sabon ranar Dimokradiyya da aka gabatar a kasar Najeriya, watau 12 ga watan Yuni, wanda a kowace shakara ya zan dole a tuna da ranar da kuma bada hutu don hidima da ta dace.

A karshe shugaban ya bada kalmar godiya ga shugabannai da kasar waje, manya a gida da yadda suka fito duka ga halartan zaman Liyafar.

Kalli hotuna a kasa;