An Sace Uwar Yahaya Muhammad, dan Majalisar Wakilai a Jihar Jigawa | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

An Sace Uwar Yahaya Muhammad, dan Majalisar Wakilai a Jihar Jigawa

Published

Ratohon da ke isa ga Naija News Hausa ya bayyana da cewa wasu Mahara da Bindiga sun sace tsohuwar dan Majalisar Wakilai a Jihar Jigawa, Yayaha Muhammad.

An sace Tsohuwar dan Majalisar ne da ke wakilcin yankin Suletan Karkar da kuma tsohon Mashawarci ta musanman a lamarin Siyasa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar, a daren ranar Litini da ta gabata.

Kwamishanan Jami’an Tsaron Jihar, Bala Zama ya gayawa gidan Talabijin yada Labarai ta Channels Television da cewa mahara da bindigar sun sace tsohuwar matan ne a nan gidanta da ke a Danladin Gumel, karamar hukumar Suletankarkar ta jihar.

Ya kuma yi alkwari da cewa hukumar su zasu yi kokari da daukar mataki ta musanman kan gano da kuma kwato matar daga hannun ‘yan ta’addan a duk inda suka tafi da ita.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina sun Ceci Mata 10 daga hannun ‘Yan Fashi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan Sandan Jihar, ASP Anas Gezawa, ya bayyana da cewa ‘yan hari da bindiga sun mamaye kauyen Wurma da ke karamar hukumar Kurfi a inda suka sace wasu mata 15, a cikin su ne kuwa tare da diyar Hakimin kauyan da kuma surukin sa daya.

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.