Connect with us

Labaran Najeriya

Karya ne! Bance Buhari ya bayar da daman takaran shugabanci Iyamirai a shekarar 2023 ba – Lawal

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sabon shugaban Sanatocin Najeriya da aka rantsar a zaben makon da ta gabata, Sanata Ahmed Lawan yayi watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizon nishadi da zancen ya furta da bakin sa cewa Jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari su bayar da daman neman takaran shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2023 ta gaba.

Ka tuna cewa rahotannai, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa da safiyar yau da cewa Mista Lawan ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari da bayar da daman fita tseren takara ga zaben shugabancin Najeriya a shekarar 2023 ta gaba.

“Na karbi rahoto da akan yadda sunana ya mamaye layin yanar gizo da zancen cewa ya gargadi shugaba Buhari da bayar wa Iyamirai daman fita tseren takaran shugaban kasa a zaben 2023 ta gaba. wannan ba gaskiya bane, matsalar rashin fahimta da bincike ne ya jawo hakan” inji shi.

A bayanin Sanata Ahmed a yayin da yake bada haske ga zancen, ya fada da cewa lallai an samu matsala ne daga sunan wanda yayi furcin.

Ya fada da cewa “Lawan da ya furtan kalamar sakatare ne ga Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, kuma inda aka samu matsalar rashin fahimtar, sunana ya zan daya da ta shi”.

Kalli sakon a Turance kamar yadda Sanata Ahmed ya tura a layin Twitter;