Connect with us

Uncategorized

An sanar da ranar da za a fara koyaswa ga ‘yan N-Power ta sashen [N-Creative]

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rukunin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke jagorancin hidimar zuba jaruruka ta hanyar fasaha, N-Power ta sanar da ranar da zasu fara bada koyaswa ga wadanda sunayan su ya fito ga sashen N-Creative a fom da suka cika a kwanakin baya.

Naija News Hausa ta gane da sanarwan ne bisa wata rahoto da aka bayar a yau Talata, 18 ga watan Yuni 2019 ga manema labarai.

Gidan labaran nan tamu ta tuna a baya da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta Tarayya ta sanar a watan Afrilu da ta wuce da amince ga bayar da kudi naira miliyan N977.7 ga wadanda sunan su ya fito a sashen rukunin aikin N-Power ta N-Creative da ta N-Tech.

An bayyana hakan ne daga bakin Ministan Kasafi da Kadamarwan Tarayya, Sanata Udo Udoma, a lokacin da yake wata gabatarwa a taron Majalisar Jiha da aka yi a birnin Abuja, a jagorancin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a fadar shugaban kasa.

Bisa sanarwan da aka bayar a yau Talata, hidimar koyaswa ta N-Creative zai fara ne ga ma’aikatan daga ranar Jumma’a, 5 ga watan Yuli ta 2019.

Haka kazalika shugabancin aikin Npower ta sanar a rahoton da cewa al’ummar Najeriya suyi la’akari da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo da cewa Npower ta fito da fom na daukar ma’aikata a shekarar 2019.

“Ba gaskiya bane, kuyi watsi da duk wata zancen cewa an fara cika fom na Npower. Idan hakan ya tabbata, zamu sanar da ku a layin yanar gizon mu” inji shugaban Hukumar.

KARANTA WANNAN KUMA; Takaitaccen Tarihi da Asalin Hausawa a Afrika