Uncategorized
Karanta bayanin Rektan Polytechnic na Yola game zancen iske Makamai a Masallacin makarantar
Hukumar kadamarwa ta makarantar Jami’ar Adamawa State Polytechnic Yola sun karyace zancen da ya mamaye layin yanar gizo, musanman wada aka sanar a gidan labaran National Daily da cewar an gane da miyagun makamai a Masallacin da ke a cikin makarantar.
A wata ganawa na tattaunawa da aka yi ranar Talata da ta gabata a Yola, Rekta na makarantar, Farfesa Abubakar Umar, ya gabatar da rashin amincewa da zancen, da cewa zancen ba gaskiya bane, “wanda ya sanar da hakan kokari yake ya bata suna da adalcin Jami’ar” Mista Umar.
“Wanda ya watsar da wannan bayanin kokari kawai yake ya tada farmaki tsakanin Kiristoci da Musulumai da ke a Jami’ar.”
Ya bayar da cewa tun lokacin da aka sanar da zancen, ya karbi kira daga hukumomin tsaro daban daban da manya a kasar akan al’amarin.
“Matakin da aka dauka na kulle Masallacin da ke a cikin jami’ar bashi da wata liki da zancen makami ko wata abu kama da hakan. An kulle masallacin ne bayan da aka karbi rahoton cewa wasu daga waje na shiga cikin masallacin da dare don kwanciya”
Rektan ya kara da cewa lallai ya karbi rahoto daga mai jagorancin tsaro makarantar da cewa wasu da ba a san da su ba na shigowa daga wajen makarantar don kwanci dadare a cikin masallacin.
“Da na gane da hakan kuma sai na umurci shugabannan MSS da ke jagorancin masallacin da su rika kulle masallacin idan sun kamala sallar dare da suke yi a kullum”
Mista Umar ya gargadi manema labarai da rinka yin bincike da kyau tare da binbini kamin su sanar ko watsar da duk wata labari da suka karba.
KARANTA WANNAN KUMA; An katange Makarantan Jami’ar Fasaha ta Rufus Giwa da shiga Yajin Aiki