Labaran Najeriya
‘Yan Fashi sun sace Dayo Adewole, yaron tsohon Ministan Kiwon Lafiya
Mahara da bindiga sun sace Dayo Adewole, yaron tsohon Ministan Kiwon Lafiya a shugabancin Muhammadu Buhari ta farko, Farfesa Isaac Adewole.
Rahoto ya bayyana da cewa an sace Dayo ne a cikin gonar sa da ke a Iroko, kusa da shiyar Fiditi, a karamar hukumar Afijio ta Jihar Oyo missalin karfe 6pm na maraicen ranar Talata.
Mazaunan shiyar sun karbi sanin hakan ne daga daya cikin ma’aikata ga Dayo da ya samu tsira daga harin. A gurguje kuma aka watsar da ‘yan farauta a dajin Iroko, a jagorancin wakilin Oniroko.
A yayin da suke binciken, ‘mafarautan sun gana da motar ‘yan fashin a kan hanyar Iware, wata kauye da ke a kusa da Iroko.
Ko da shike ba a gane inda barayin suka tafi da Dayo ba, amma tugumar cewa wata kila barayin sun sake motarsu ne bayan da suka gane da cewa sanarwa sace Dayo ya kai harga gidan radiyo a take.
Har yanzu ana kan binciken inda aka shigar da Mista Dayo.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Barayi sun kashe ‘yan Kabu-Kabu biyu a Jihar Kaduna a Yau.
Daya daga cikin ‘yan kabu-kabu da barayin suka hara, Rayyanu Yahaya Dawakin Tofa, ya bayar ga manema labarai da cewa harda shima an kwace masa wayar salula da kudin da yake tare da shi.