Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 21 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 21 ga Watan Yuni, 2019

1. Abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa Osinbajo, gwamnonin a wajen hidimar NEC

Shugaba Muhammadu Buhari ya kalubalanci sabbin kwamitin tattalin arziki na kasa (NEC), wanda zasu yi jagorancin daga shekarar 2019 zuwa 2023 a fadar shugaban kasa, Abuja, da cewa su tabbatar da fidda sabon tsarin tattalin arziki wanda zai karfafa harkokin kasuwanci kasar.

Naija News ta fahimta da cewa Shugaban kasan a isarsa majalisar a missalin karfe 1.23pm, ya bukaci sabin ‘yan hukumar NEC da ci gaba da bin manufofi masu muhimmanci da kuma mayar da hankali ga tsaro, ilimi da aikin noma.

2. Ka dakata da Karbar ‘ Yan Adawan shugaba Buhari – APC sun kalubalanci shugaban Majalisar Dattijai

Kwamitin Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar sun gargadi shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan da ya janye da sanya ‘yan’ adawar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin ma’aikatan sa.

Kungiyar sun bayyana da cewa irin wadannan matakan ya kasance abin kunya da zagi ga Shugaba Buhari da sauran mutanen da suka goyi bayansa (Lawan) don cin nasara ga zama Shugaban Majalisar Dattijai.

3. Jam’iyyar PDP zata sake dawowa da hakin ta  – inji Secondus

Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), Uche Secondus, ya umarci membobin jam’iyyar da su hada hannu don dawo da daraja da hakin jam’iyyar da aka kwace.

Secondus ya sanar da wannan ne a  yayin da yake jawabi a kwamitin NEC ta karo na 86 da suka yi a birnin Tarayya, Abuja, a ranar Alhamis da ta wuce.

4. Dalilan jinkirta wajen aiwatar da sabon albashin ma’aikata – TUC

Duk da yake ma’aikata suna tsammanin karbar sabon albashi da aka amince da kuma gabatar, akwai wasu matsaloli da ba a gama shan karfin su ba.

Naija News ta fahimta da cewa matsala da batun da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar kadamarwa ga Jama’a a kan samfurin na iya kawo jinkirta ga aiwatar da sabon Ƙankanin albashin ma’aikatan.

5. Gwamnonin ba zasu dade da bayyana hangen su ba akan ‘Yan Sandan Jiha – Fayemi

Kayode Fayemi, Shugaban Hukumar Gwamnonin Najeriya (NGF), ya ba da wata sanarwa game da amincewar Gwamnonin kan kafa ‘yan sandan Jiha.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Abuja, a lokacin ganawar a karkashin jagorancinsa, Fayemi ya bayyana  cewa gwamnonin ba su yanke shawara kan kafa ‘yan sandan jiha ba tukuna sabili da karfin asusun jihohin duka ya banbanta.

6. Lawan ya tsige Festus Adedayo da ya sanya ga matsayin mataimakin sa ga sadarwa

Shugaban majalisar dattijai na 9, Sanata Ahmed Lawan, ya janye aikin da ya baiwa Dakta Festus Adedayo na matsayin mai bada shawara na musamman a kan hanyar sadar da labarai ga jama’a.

Naija News Hausa ta gane da cewa Sanata Lawan yayi hakan ne don biyayya ga gargadi da sauran ‘yan majalisu na jam’iyyar APC suka bashi akan sanya tsohon ma’aikaci ga Sanata Bukola Saraki a karkashin sa.

7. Abin da NEC suka Tattauna game da Tsaro da kuma zancen Almajiranci

Babban Mashawarcin Tsaro na kasa, Babagana Monguno ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta haɓakar da ƙungiyar Al-majiri hade da wasu.

Ya gabatar da hakan ne ga wakilan majalisar dokokin jiha a ƙarshen taron Hukumar NEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.

8. Shugaba Buhari ya nada sabon Janar Manajan Kamfanin NNPC

Naija News Hausa ta samu tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon darakta na rukunin kamfanin tsufurin Man Fetur ta NNPC na Najeriya.

Buhari ya nada Mr Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban NNPC wanda zai maye gurbin Dokta Maikanti Baru.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com