Connect with us

Uncategorized

Hukumar NAHCON ta rage ga Kudin zuwa Hajj ta 2019 (Karanta ko nawa aka rage)

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Tafiya zuwa ga Hidimar Hajj ta Najeriya (NAHCON) tayi binbini akan kudin tafiya zuwa kasar Makka, ta kuma gabatar da rage tsadar kudaden da ake biya.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta bayar akan hidimar tafiyar zuwa Hajj ta shekarar 2019.

“Hukumar NAHCON tayi binbini ga diban rage yawar kudade da ake biya da ya kunshi zagaye-zagaye da ‘yan Najeriya da zasu tafi kasar Macca don hidimar Hajj zasu yi a kasar Saudi don hidimar Hajj da Umrah” inji Fatima.

A cikin sanarwan, an bayyana da cewa hukumar ta rage Riyals 620 a tsarin kudin kasar Saudi, wanda a kimance ya kama Dala 165. “Wannan ci gaban zai shafi dukan jihohin kasar ne har matafiya daga birnin Tarayya.”

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hukumar ta rage Naira dubu N51,170.45 a lissafin kudin Najeriya daga yawar kudin da ake biya ga hukumar a da don hidimar Haji.

An kuma sanar ga dukan jihohin kasar da sanar ga matafiya da kuma tabbatar da mayar da naira N51,170.45 ko dukan wadanda suka rigaya da biyan kudin su kamin aka gabatar da rage tsadar kudin.

Naija News Hausa ta kula da cewa idan an cire Naira N51,170.45 daga cikin kudin da da aka gabatar, kudin zuwa Babban Haji a yanzu zai kama N1,508,824.55, karamin Haji kuma zai kama N1,462,627.65.

An kuma sanar da kara daga ranan rufe biyan kudin zuwa Hajj ta shekarar 2019 zuwa ranar 15 ga watan Yuli ta gaba.

Hukumar kuwa ta gargadi dukan matafiya zuwa Hajj ta bana da tabbatar da karshe biyan kudaden su da kuma bayar da dukan takardu da abubuwar da ake bukata don tafiyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi barazanar kame duk yaron da aka gane da yawace-yawacen banza a Jihar, da ya ki ko ta ki zuwa makarantan Boko.

“Roko da yawace yawace ba al’adar Musulunci bane” inji Ganduje.