Boko Haram sun kashe mutane 20 a sabuwar hari da suka kai Ngamgam, Borno

Naija News Hausa ta karbi sabuwar rahoto da harin Boko Haram a shiyar Ngamgam

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a shiyar Ngamgam, kilomita 50km ga Damasak, a nan karamar hukumar Mobbar, inda suka kashe akalla mutane 20.

Niaja News Hausa ta fahimta kamar yadda aka bayar a sanarwan da cewa ‘yan ta’addan sun iske mutanen ne a yayin da suke kan aiki a gonar su, suka kuma kashe su nan take.

Mugun harin da ya faru a ranar jiya ya kara tsorata mazaunan yankin kwarai da gaske, ganin irin yadda ake kashe rayuka mutane kamar dabbobi.

Mun sanar a Naija News Hausa ‘yan sa’o’i da suka gabata yadda mutanen Tiv da Jukuns suka shiga wata farmaki da har aka kashe mutum guda a Jihar Taraba.