Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 27 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 27 ga Watan Yuni, 2019

1. Shugaba Buhari da shugaban Majalisar Dattijai sun gana a Aso Rock

A ranar Laraba, 26 ga watan Yuni da ta wuce, shugaban Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban sanatocin Najeriya, Ahmed Lawan, a nan fadar shugaban kasa ta birnin tarayya, Abuja.

Naija News Hausa ta gane da cewa Buhari ya ja shugaban sanatocin ne zuwa tattaunawar kofa kulle, a misalin karfe 3:25pm ta ranar Laraba.

2. Kotu tayi watsi da karar da aka gabatar ga AbdulRazaq, Gwamnan Jihar Kwara

Kotun Koli da ke a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a ranar Laraba da ta wuce ta gabatar da hukuncin yin watsi da karar zargin rashin cikakken takardan takara da aka gabatar ga AbdulRahman AbdulRazaq, Gwamnan Jihar Kwara.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Kotun tayi hakan ne bayan da mai gabatar da karar ya bayyana janye zargin.

3. Zamu tada kai tsaye ga hukuncin kotun koli ta Zamfara  – APC

Rukunin Jam’iyyar shugabancin kasa, APC ta Jihar Zamfara sun yi barazanar kalubalantar hukuncin Kotun koli game da Jam’iyyar su da kuma ‘yan takaran su.

Jam’iyyar sun bayyana hakan ne a bakin Ciyaman na Jam’iyyar APC ta Jihar, Alhaji Lawali Liman, a wata gabatarwa da yayi a sakateriyar Jam’iyyar da ke a Gusau, ranar Laraba da ta wuce.

4. Lawan ya goyi bayan IGP na Jami’an tsaro

Shugaban Sanatocin Najeriya, Ahmed Lawan ya bayyana goyon bayan sa ga bukatar shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu akan gabatar da kadaitacen Asusu ga Kwamishanonin hukumar tsaron a dukan Jihar 36 ta tarayyar kasar.

Lawan ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata ziyara da IGP ya kai masa.

5. Boko Haram sun kashe Manoma 20 a garin Borno

Wasu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a Ngamgam ta Jihar Borno, inda suka kashe manoma kimanin 20, a nisar kilomita 50km ga Damasak, nan karamar hukumar Mobbar.

An kashe manoman ne a yayin da suke kan aiki a gonakin su.

6. Ban bar asusun Jihar Zamfara da wata bashi ba  –  Yari

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari yayi barazana da bugun gaban cewa bai sauka jagorancin jihar Zamfara da wata bashi ba.

Naija News Hausa ta gane da cewa Yari ya fadi hakan ne da cewa bai bar sabon Gwamnan Jihar, Bello Matawalle da wata bashi ba.

7. An kashe mutane 5, Kone gidaje kuma a wata farmaki a Taraba

Farmaki da ya tashi a Jihar Taraba ranar Talata da ta gabata tsakanin Tiv da Jukuns a karamar hukumar Rafinkada, ya tafi da rayuka 5 da kone konen gidaje.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne a bayanin Mista Daniel Adidas, Ciyaman na masu kula da zamantakewar gida-da-gida a yankin.

8. Mahara da Bindiga sun Sace Matafiya a hanyar Akure-Ado

Wasu ‘Yan Hari da Bindiga da har yanzu ba a gane da su ba, a ranar Talata da ta gabata sun sace kimanin mutane 28, matafiya da ke kan tafiyar a wata hanya da ke a Ado-Akure, Jihar Ondo.

An bayyana da cewa yanayin lalacewar hanyar ne ya sa maharan suka sami sauki da nasarar tare motocin.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com