Connect with us

Uncategorized

Kalli Abin da Sojoji suka yiwa wani Sojan Karya da aka kama da zaluntar mutane

Published

on

at

Sojojin Najeriya sun kame wani Sojan Karya

Wani matashi da ya saba zaluntar mutane a sunan cewa shi soja ne ya fada a hannun Sojojin Gaske a Jihar Osun.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa matashin da har yanzu ba a gane da ainihin sunansa ba, ya saba tsorata da zaluntar Dalibai a Makarantan Fasaha ta Igbajo Polytechnic a Jihar Osun.

Hausawa sun ce “Kulluma na barawo amma rana daya ga mai kaya”, Sojan karyan ya fada a hannun rundunar Sojojin Jihar, inda suka ci mutuncin sa a fili ga ganin jama’a.

An bayyana da cewa matashin kan sanya kakin Sojoji ne, sai ya haura ga shiyar Makarantan Jami’ar, daga nan kuma sai yayi ta cin mutunci dalibai a sunan Soja.

Sojojin kuma da suka kama shi sai suka Isgila shi da yi masa mugun duka a gaban jama duka.

Kalli Bidiyon a kasa;

https://www.instagram.com/p/BzcbvWkH-Ww/?utm_source=ig_embed

KARANTA WANNAN KUMA; Bayanin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar game da Sanata Elisha Abbo da ya zalunci wata Mata a birnin Abuja