Connect with us

Uncategorized

Hadarin Motar Tanki ya dauke ran wani a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton wata hadarin Motan Tanki da ya fashe da gobarar wuta a wata shiya a Jihar Kano.

Manema labarai sun bayyana da cewa mutun guda ya rigaya da mutuwa a fashewar Motar da wuta, a yayin da kuma mutun guda ya sami mumunar rauni. An bayyana da cewa hadarin ya faru ne a shiyar hanyar Rano, a yankin Bunkure ta karamar hukumar Bunkure, a Jihar Kano.

Kakakin yada yawun hukumar Yaki da Gobarar Wuta da a Turance aka kira da Fire Service ta Jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed, ya bayyana ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) da ke a Jihar Kano da cewa abin ya faru ne a misalin karfe 8:52 na safiyar ranar Alhamis.

“Mun karbi wata kirar gaggawa ne daga wani mutumi mai suna Malam Mohammed a misalin karfe 8:52 na safiyar ranar Alhamis da cewa wata Motar Tanki da ke dauke da man fetur ya fashe da gobarar wuta a hanyar Rano.”

“Da karban kirar, ba tare da jinkiri ba sai hukumar ta aika da ma’aikata da motoci don lafar da yanayin da kumar ribato rayuka” inji Mohammed.

Mista Mohammed ya bayyana da cewa basu iya gane lambar motar tankin da kyau ba a yayin da gobarar wutan ya lalatsa filetin motar.

Ya kuma bada haske da cewa hukumar ta iya gane da cewa hadarin motar da ya kai har ga gobara ya faru ne sanadiyar yawan gudu da direban ke yi a kan babban hanyar.

Shugaban hukumar ya gargadi direbobi masu tuki da rage yawar gudu a yayin da suke tuki a kowani lokaci.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da wata hadarin motar man fetur da ya tafi da rayuka akall 37 da barin mutane 101 da mumunar raunuka a Jihar Benue.