Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 5 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 5 ga Watan Yuli, 2019

1. Shugaba Buhari ya gana da shugaban Hukumomin Tsaro

A ranar Alhamis da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari yayi wata zaman kofa kulle a cikin Aso Rockk tare da manyan shuwagabannan hukumomin tsaron kasa.

Naija News ta fahimta da cewa taron ba zai wuce tattaunawa akan matsalar hare-hare da sace sace da ake fuskanta a kasar ba.

2. Farfesa Nwabueze ne ya jagorancin rukunin neman Yanci ga Atiku a Kotu

Tsoho Lauya da kuma sanane Farfesa mai shekarun haifuwa 87, Ben Nwabueze ya halarci gaban Kotun Hukunci zabe a ranar Alhamis da ta wuce don jagoran karar dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar.

Hakan ya kasance ne a yayin da Atiku da Jam’iyyar PDP ke gabatar da shaidu ga rashin amincewa da sakamakon zaben watan Fabrairu.

3. Matasan Arewa sun kalubalanci Osinbajo, Obasanjo da Buhari akan kafa Ruga cikin

Wata rukunin Matasan Arewacin Najeriya a karkashin kungiyar Hadayar Matasan Arewa (CNG), sun yada yawu akan matakin gwamnatin Tarayya game da batun kafa Ruga.

Rukunin Matasan, a yayin da suke wata ganawa a ranar Laraba da ta wuce, sun bayar da tsawon kwanaki 30 ga shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar da kafa hidimar Ruga a jihohin kasar Najeriya.

4. Gbajabiamila ya nada Doguwa a matsayin jagoran gidan Majalisar wakilai

Kakakin Yada yawun Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya gabatar da Ado Doguwa, dan majalisa da ke wakilcin Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar APC, a matsayin jagoran babban rukunin Majalisar wakilai.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a sanarwan da Gbajabiamila ya bayar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli, anan birnin Abuja.

5. Kaduna: Gwamna El-Rufai yaci nasara ga kara a Kotu

Kotun Kolin Tarayya ta Jihar Kaduna ta gabatar da hukunci akan kara da kalubalanta da ake ga Nasiru El-Rufai, a matsayin dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, a karkashin Jam’iyyar APC ga zaben Gwamnoni ta shekarar 2019.

Kotun ta bada tabbacin nasara da amince da El-Rufai a matsayin gwamnan Jihar Kaduna daga Jam’iyyar shugabancin kasa, APC.

6. Kotun Kara ta karbi shaidu 883 daga Atiku

Dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a halin yanzu ya bayar da shaida 883 daga Jihar Neja ga Kotun Hukuncin zaben.

Naija News fahimta da cewa hakan ya faru ne a yayin da dan takaran ke cika alkawarin sa na bayar da shaidu don bada tabbacin cewa ba shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 ba.

7. Kotun Koli na shirye don gabatar da hukunci akan zaben Jihar Osun

Kotun Koli da ke jagorancin karar zaben kujerar Gwamna ta Jihar Osun da aka yi a shekarar 2018, na a shirye don gabatar da hukunci ta karshe akan karar.

Gabadin hakan, Hukumar ‘Yan Sandan Jihar, a ranar Alhamis da ta gabata ta gargadi mazaunan Jihar da tabbatar da halin sulhu tsakanin su, da kuma janye daga halin tanzoma.

8. PDP sun ki amince da zabin da Gbajabiamila yayi ga jagoran karamin majalisa 

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP sun bayyana rashin amincewarsu da matakin kakakin yada yawun Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, akan zabin da yayi ga mai jagoran karamar majalisa.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Gbajabiamila ya rantsar da Ndidi Elumelu a matsayin jagoran karamar majalisar wakilai, da kauracewa zabin da PDP tayi ga Kingsley Chinda.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com