Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Bam ya tashi da Sojojin Najeriya a Chibok

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani Jami’in Sojan Najeriya ya rasa ransa a wata Bam da ‘yann ta’adda suka haka a Chibok.

A ranar Alhamis da ta gabata, wata rukunin darukan Sojojin Najeriya ta 117 task force da ke a Chibok sun ci karo da wata Bam na (IED) da ‘yan ta’adda suka haka, a yayin da suke kan komawa hedikwatan su.

Bisa bayanin da manema labaran TheCable suka bayar, sun bada haske da cewa abin ya faru ne a misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Alhamis da ta wuce, bayan da darukan yakin suka bar Kwamdi da haurawa zuwa garin Chibok da, kilomita 12 da inda suka baro, da ratsawa ta hanyar Dogon Dajin Sambisa.

Bincike ya nuna da cewa ‘yan ta’addan sun haka bam din ne tun da tsakar daren ranar Laraba. Bam din kuma ya tashi a isar Sojojin Najeriya wajen da aka haka shi, nan take ya dauke ran mutun daya da kuma barin akalla mutane Uku da mugun rauni.

Mai bada labarai ga game da lamarin ya bayyana da cewa an rigaya an kai mutane Uku da suka sami raunuka a asibitin da ke a Yola, da kuma gabatar da cewa dole sai da aka aiko da sabbin sojoji don taimaka wa sauran Sojojin a yayin da suka kasa ga karfin mayar da hari.

A lokacin da aka bayar da wannan rahoton, ba a samu karban bayani ba daga bakin Col. Sagir Musa, kakakin yada yawun rundunar sojojin ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Sojojin Najeriya sun kame wani Sojan Karya a Jihar Osun.
An bayyana da cewa matashin kan shiga shiyar Makarantan Fasaha ta Igbajo Polytechnic da ke a Jihar Osun ne don tsoratar da zaluntar Dalibai, a sunan cewa shi Soja ne.