Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na bukatar Addu’a – inji TB Joshua

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba da jagoran Babban Ikilisiyar ‘Synagogue Church of All Nations (SCOAN), Annabi TB Joshua, ya gargadi ‘yan Najeriya duka da su cika da yiwa shugaba Muhammadu Buhari addu’a a koyaushe.

Sananan Annabin ya fadi hakan ne a yayin da yake wa’azi a hedikwatan Ikilisiyar sa da ke a Ikotun Egbe, Jihar Legas, ranar Lahadin da ya gabata.

A bayanin TB Joshua, ya bayyana da cewa addu’ar zai kunshi rokon Allah da baiwa shugaba Muhammadu Buhari hikima da ganewa wajen jagorancin kasar Najeriya yadda ya dace.

Ya ce “Ina tsaye a yau da sanar maku da ganin wahayi da nayi a makonnai biyu da suka gabata akan kasar Najeriya, da aka sani da bugun gaban Afrika”

“Bari muyi wa gwamnatin kasar addu’a, da kuma shugaba Muhammadu Buhari. babu mutumin da ya cika a fadin duniya”

“Mu roki Allah na sama da katange shi da kuma cika shi da hikima da zai iya jagorancin kasar da ita, a yadda ya kamata”

“A wahayi na, na ga seraphim (taron mala’ikai) suna saukowa da ruwa daga sama. Ruwar kuma na sauka da sabontaka a kasa da kwanciyar hankali. Al’ummar Najeriya, bari mu cika da addu’a”

KARANTA WANNAN KUMA; Majalisar Dokoki sunyi Alkawarin kafa baki ga neman a saki El-Zakzaky daga Fursuna.