Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 9 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, Talata, 9 ga Watan Yuli, 2019

1. Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Nijar

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga ziyarar da ya kai a kasar Nijar, wajen wata hidimar tattaunawa ta hadayar kasar Afrika, da aka fi sani da African Union (AU) ta goma shabiyu (12th) da aka yi a Niamey, Niger.

Naija News ta fahimta da cewa jirgin da ya dauko shugaba Buhari ya sauka ne a Filin jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke a Abuja, misalin karfe biyu na tsakar ranar Litini da ta gabata.

2. Atiku da PDP sun tsorata Buhari a yayin da suka gabatar da shaida ta farko a Kotu

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP da dan takaran su ga kujerar shugaban kasa ta shekarar 2019, Atiku Abubakar, sun fara gabatar da shaidu a kotun neman yanci don kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta samun sanin cewa Buba Galadima, sananan jigo a Jam’iyyar PDP da ya saba kalubalantar shugabancin Buhari ne shaidar farko da PDP suka fara gabatarwa.

3. Ma’aikacin Hukumar INEC ya bayyana yadda INEC ta samar da sakamakon Zaben 2019 a kan Kwamfuta

Wani ma’aikacin hukumar gudanar da hidimar zaben Najeriya (INEC) ga zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Mista Adejuyitan Olalekan, ya gabatar da yadda hukumar tayi anfani da na’urar Kwamfuta wajen ajiye sakamakon zaben shugaban kasa ta 2019.

Ya bayyana hakan ne ga Kotun Neman yanci a ranar Litini da ta wuce a birnin Abuja, da cewa sakamakon zaben yankin su ne kawai ya samar akan kwamfuta.

4. Sanata Abbo ya ki amince da laifin sa a Kotu

Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa, Sanata Elisha Abbo, ya bayyana kin amincewa da laifin da ake zargin sa da shi na zaluntar wata mata a Abuja.

Elisha ya bayyana hakan ne a ranar Litini, a lokacin da Jami’an tsaron birnin Tarayya, Abuja, suka gabatar da shi a gaban kotun Majistare ta Zuba.

5. Galadima ya bayyana dalilin da yasa yake kalubalantar Buhari a kullum

Alhaji Buba Galadima, Dan Siyasa da kuma kakakin yada yawun neman zabe ga Atiku a zaben shugaban kasa ta 2019, ya bayyana dalilin da yasa yakan kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari.

Galadima ya bayyana dalilin ne a yayin da yake gabatarwa a gaban kotun kara don bayar da shaida da karyace nasar Buhari a zaben 2019.

6. APC/PDP: Karya ne zancen cewa ba a ajiye rahoton zabe a na’urar kwamfuta ba – Ma’aikacin INEC

A yayin da PDP ke gabatar da shaidun su akan hidimar zaben shugaban kasa ta 2019, mai bada shaidar jam’iyyar ta biyu, Peter Uzioma Obi, a ranar Litini ya gabatar da cewa karya ne da cewa INEC bata samar da sakamakon zaben a kan kwamfuta ba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Obi ya tsayawa Atiku Abubakar ne don kalubalantar nasarar Buhari a Kotu.

7. Farfesa Yakubu yayi alkawarin bada haske ga hidimar zaben 2019

Bisanin gwagwarmayan da jayaya da ake da hukumar gudanar da hidimar zaben Najeriya (INEC), Ciyaman na hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, yayi alkawalin bada haske ga al’amarin zaben bayan Kotu ta gama binciken ta.

Ka tuna da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar a baya, yayi karar Jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari a kotu akan rashin amincewa da zaben watan fabrairu.

8. Hukunar ASUU sun kalubalanci shugaba Buhari akan rashin bada hadin kai ga Ilimin Kimiya

Hadaddiyar Kungiyar Malaman Makarantar Jami’a Babba, da aka fi sani da ASUU, a karshen makon da ta gabata, sun kalubalanci gwamnatin tarayya da cewa ya kamata su gwamnatin tarayya ta karasa ga bayar da isashen kudi ga hidimar makarantu.

A cikin bayanin kungiyar, sun kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da cewa yadda yake tafiyar da gwamnatin sa zai iya raunana ci gaban Makarantun Jami’a da ke a kasar.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shadin Hausa.NaijaNews.Com