Connect with us

Uncategorized

Hukumar Tsaron Jihar Ogun sun kame Makiyaya 3 da kashe wani dan shekaru 40

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron Jihar Ogun sun bayyana da kame wasu mutane Uku da aka gane da zama makiyaya Fulani da zargin kashe wani Manoni, Rafiu Sowemimo, mai shekaru 40 ga haifuwa.

Naija News ta sami fahimtar cewa makiyayan sun kashe mutumin ne a shiyar Adao, anan kauyan Alabata, jihar Ogun.

Bisa rahoton da manema labarai suka gane da ita, sunan makiyayan na kamar haka; Muhammed Adamu, Saliu Ismail da kuma Saliu Adamu.

An bayyana da cewa makiyayan sun shigar da shanaye da tumakin su ne a cikin gonar marigayi Sowemimo, suka kuma lalatar da hatsin gonar.

“A yayin da Sowemimo yayi kokarin hana su hakan, sai suka hare shi da wuka, suka kuma kuma soke shi har ga mutuwa”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Hari da Makami sun sace Maman Siasia, tsohon Kocin ‘yan wasan kwallon Najeriya.