Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 19 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 19 ga Watan Yuli, 2019

1. IMN ta kalubalanci Kotun kara da kin amince da sake El-Zakzaky da Matarsa

Bayan da Kotun Koli ta jihar Kaduna ta ki sakin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky daga kurkuku, a ranar Alhamis, kungiyar harkar musulunci ta Nigeria, wanda aka fi sani da Shi’a, sun bayyana cewa shugabansu na kusa da makanta kuma yana iya rasa rayuwansa idan ba a yarda da ya je binciken lafiyar jikinsa ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Ciyaman kwamitin neman yanki ga El-Zakzaky, Abdurrahman Abubakar Yola ya rattaba hannu.

2. INEC ta samar da takaddun da Jam’iyyar PDP ta bukata a kotu

Hukumar gudanar da hidimar zaben kasar Najeriya (INEC), ta samar da wasu daga cikin takardun da Jam’iyyar PDP da kuma dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar suka bukaci hukumar da bayar wa.

Naija News ta tuna da cewa Kotun koli ta kasa da kasa a ranar Laraba da ta wuce, ta umarci hukumar INEC da gabatar da takardun zuwa ga masu sauraro a ranar Alhamis din nan.

3. CAF ta Tsige Amaju Pinnick A matsayin mataimakin shugaban hukumar

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), Amaju Pinnick ya janye daga matsayinsa na mataimakin shugaban hukumar kula da kwallon kafa na Afrika (CAF).

Naija News Hausa ta fahimta da cewa bayan da aka dakatar da Mista Pinnick, a kuma sanya Mista Danny Jordaan daga kasar South Afrika don ya maye gurbin Pinnick.

4. Shugaba Buhari ya gana da Ooni Of Ife

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Alhamis da ta gabata, ya karbi ziyarar Ooni na Ife, Mai Martaba, Sarki Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II.

Ooni na Ife ya isa gidan shugaban kasa ne a ranar Alhamis din nan da ta wuce a birnin tarayya.

5. Mikel Obi ya huta daga buga kwallon kafa na duniya

Tsohon dan wasan Chelsea da kuma kyaftin din Super Eagles, Mikel Obi ya sanar da ritaya daga kwallon kafa na kasa da kasa tare da tawagar Najeriya.

Naija News Hausa ta kula da cewa ritayar Mikel ya biyo ne bayan da Super Eagles ta lashe lambar zinare a gasar cin kofin Afrika ta 2019 (AFCON).

6. ‘Yan hari da bindiga sun kashe Sojojin Najeriya biyu a Akwa Ibom

Wasu ‘yan hari da makami da ba a gana dasu ba sun kashe sojoji biyu kuma da sace wani kwarararen ma’aikaci a yankin Ukanafun, watau karamar hukumar a Jihar Akwa Ibom.

Naija News Hausa ta gane da cewa mutumin da aka sace, babban ma’aikaci ne a kamfanin Al Madal, da cewa an sace shi ne a yayin da yake zagaya da binciken aikin da ake a shiyar Ikot Ibritam, da kuma hanyar Inen Ekeffe da Odoro Ikot zuwa hanyar Ukanafun a ranar Laraba, Yuli 17.

7. Majalisar Dattijai ta tabbatar da zaɓen Buhari

Majalisar Dattijai ta Najeriya a ranar Alhamis ta tabbatar da kwamishinoni hudu na Hukumar sadarwa na Najeriya (NCC).

Ka tuna da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunayensu zuwa ga majalisar dokokin Najeriya ne a baya, don tabbatar da su.

9. Cikakken bayani game da wanda ya cire Tsarin Na’urar kwamfuta ta hukumar INEC

Reno Omokri, tsohon ma’aikatci ga tsohon shugaban kasar Najeriya, ya yi zargin cewa wani Femi Taiwo ne ya fitar da sakamakon zaben da hukumar INEC ta boye akan na’urar kwamfuta ta hidimar zaben 2019.

an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da aka yi amfani da shi a lokacin zaben 2019.

Ka tuna da cewa Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 na kalubalantar sakamakon zaben 2019 da nasarar Muhammadu Buhari a zaben.

Ka sami kari da cikkaken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com