Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 24 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 24 ga Watan Yuli, 2019

1. Shugaba Buhari Ya aika da Jerin sunan Ministoci ga Majalisar Dattawan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tsawon kwanaki 50 akan karagar mulki a wa’adi na biyu, a karshe ya aikar da jerin sunayen ministoci ga majalisar dattawa don tantancewa.

Naija News ta tuna cewa a baya majalisar dattijai ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ranar Juma’a domin gabatar da jerin sunayen ministocin domin tantancewa.

2. Gidan Majalisar Wakilai na cikin Cece-kuce akan Jagoran ‘yan Shi’a

Majalisar Wakilai ta cike da cece-kuce a ranar Talata bayan wani dan majalisar yayi kiran da a saki Ibrahim El-Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wanda aka fi sani da Shi’a.

Naija News Hausa ta tuna da cewa kimanin mutane 12 ne aka ruwaito sun mutu bayan zanga-zangar nuna rashin jin dadi da ‘yan kungiyar shi’a suka yi a Abuja, ranar Talata da ta gabata, harma da kashe wakilin gidan talbijin din Channels Tv yayin zanga-zangar.

3. Majalisar dattijai ta dakatar da hutun shekara da shekara Don Binciken Ministocin da Shugaba Buhari ya gabatar

Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talata ta jinkirta da wucewa hutun shekara da shekara da ta kan yi, da kuma suke batun farawa a ranar Juma’a don tantance mutane da Shugaba Muhammadu Buhari ya mikar ga kujerar Minista.

Naija News ta tuna cewa a baya majalisar dattijai ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ranar Juma’a domin gabatar da jerin sunayen ministocin domin tantancewa, gazawar wanda majalisar zartarwar za ta ci gaba da hutun wata biyu.

4. Dalilin da yasa bamu yi biyayya ga Umarnin Kotu ba game da Sakin El-Zakzaky – Shugabancin kasa

Shugabancin kasar Najeriya ta sake tabbatar da dagewarsu akan tsare Shugaban ‘Yan Shi’a, Sheik Ibrahim El-Zakzaky, duk da cewa kotu ta bada umarnin a sake shi.

Mista Femi Adesina, mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya fada a ranar Talata da cewa har yanzu gwamnati ta ki bin umarnin Alkali Gabriel Kolawole kan sakin El-Zakzakky saboda bata gamsu ba tukuna da hukuncin.

5. Nabena Ya Bayyana Yadda Rashin halaka tsakanin Oshiomhole da Oyegun zai Iya Shafar Jam’iyyar APC

Mataimakin kakakin yada yawun jam’iyyar shugabanci (APC), Yekini Nabena, ya yi kira da a kawo karshen fada da ke a tsakanin shugaban jam’iyyar na tarayya, Adams Oshiomhole tsohon shugaban jam’iyyar, Odigie-Oyegun.

Nabena ya bayyana da cewa tsatsaguwa da ke tsakanin su biyun na da damar iya shafar jam’iyyar su a zabubbuka ta gaba.

6. Atiku ya kalubalanci shugaba Buhari

Naija News ta kula da cewa Jerin sunayen ministocin da shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa domin tantancewa ya zan da cece-kuce daban-daban daga al’umar Najeriya.

Daya daga cikin irin wadannan maganganu ya fito ne daga bakin Paul Ibe, Kakakin yada yawun dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar Adawa, PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

7. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya yi watsi da bukatar APC

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Mista Ahmed Lawan ya nuna yin watsi da bukatar da jam’iyyarsa, APC ta gabatar na cewar ya gayyacesu idan ya samu wata matsala tsakaninsa da kowane sanata.

Ahmed ya bayyana rashin amincewarsa ne da bukatar Jam’iyyar a lokacin da suka ziyarceshi a wata ziyara da Abba Dalori ya jagoranta, a ranar Litinin a Abuja.

8. Rashin tsaro: Shugaba Buhari na karkashin tsananci don dakatar da Shugabannin Ma’aikata

Bayan hare-hare da kashe-kashen da kuma sace-sacen mutane da ke gudana a Najeriya, an matsa lamba tsananci ga Shugaba Muhammadu Buhari don korar Shugabannin tsaro daga Ofishin su.

A wata sanarwa da Comrade Gbenga Soloki, shugaban kwamitin kare hakkin dan adam, ya fitar a Legas, ranar Litinin da ta gabata, ya ce adadin kashe-kashe da sace-sacen da ke gudana a kasar na da matukar tayar da hankali da kuma iya haifar zamantakewar kwarai a cikin kasar.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa