Labaran Najeriya
Sallar Layya: Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Daura don Sallar Eid-el-Kabir
Naija News Hausa ta sami rahoton tafiyar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a yau da barin birnin Abuja don zuwa Daura, jihar Katsina don sallar Eid-el-Kabir. Bisa rahoton da jaridar Daily Trust ta bayar, shugaban zai bar fadar Shugaban kasa ne yau a bayan sallar Juma’a.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar da hutu ga Ma’aikata da Makarantu, Kamfanoni da sauransu Hutun Sallah a baya.
Ka tuna da cewa Musulumai a dukan fadin kasar, a ranar Lahadi ta gabata za su hada hannu da takwarorinsu na duniya don yin bikin Sallah ta Eid-el-Kabir na wannan shekara 2019.
Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari bai sake shiga Daura ba tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a watannai da suka shige a kasar, wanan shakara.
KARANTA WANNAN KUMA; Takaitaccen Tarihi da Asalin Hausawa a Afrika