Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 15 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 15 ga Watan Agusta, 2019
1. Buhari ya sanya hannu kan dokar canza sunan Ofishin fursuna na Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a wata doka da ya baiyana canza sunan gidan yari na Najeriya daga Nigerian Prison Service zuwa to Nigerian Correctional Service.
An baiyana hakan ne a wata sanarwa da aka bayar daga hannun Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a harkan gidan Majalisa, Mr. Ita Enang, a ranar Laraba da ta gabata.
2. El-Zakzaky Ya Ki Amincewa Da Likitocin da bai San da su ba
Naija News ta fahimci shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da suna Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kin karban likitoci da bai san da su ba.
Rahoton da aka bayar ya baiyana da likitocin sun bambanta da wadanda aka sanya ga El-Zakzaky kamin barin sa kasar Najeriya ranar Litinin da ta gabata.
3. EFCC ta gurfanar da Surukin Atiku Abubakar
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kame Abdullahi Babalele, suruki ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma dan takarar Shugaban kasa daga jam’iyyar Dimokradiyya, a babban zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar.
Naija News ta fahimci cewa, an gurfanar da Babalele ne a ranar Laraba a gaban Mai shari’a Nicholas Oweibo a wata babbar kotun tarayya da ke a Legas, kan zargin kudade da aka fyauce na kimanin dala $140,000 a yayin babban zaben shekarar 2019.
4. Borno Ta Bayar Dajin Sambisa ga Gwamnatin Najeriya don kafa tsatsan Ruga
Gwamnatin Jihar Borno a karkashin jagorancin gwamna Babagana Umara, ta bayar da dogon dajin Sambisa da ake tsoro ga gwamnatin tarayya don shirin sasanta rikicin RUGA.
Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da suka hada da Rundunar Tsaron Civil Defence (NSCDC), Agro Rangers da mafarauta da su tabbatar da tsarin dajin.
5. Buhari ya Ziyarci sansanin IDP A Katsina
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ziyarci karamar hukumar Batsari domin nuna juyayi ga ‘yan gudun hijirar a cikin yankin.
Naija News Hausa ta fahimci cewa Batsari na daya daga cikin bangarorin takwas na karamar hukumar jihar da ke fuskantar hare-haren da ayyukan masu sata da garkuwa da mutane a jihar Katsina.
6. Asibitin Indiya ta Amince Da Bukatar El-Zakzaky
Asibitin Indiya da ke jagorantar kulawa da jagoran Harkar Ci gaban Musulunci na Najeriya (IMN), Ibrahim El-Zakzaky, sun amince da barin sanannun likitoci ga El-Zakzaky da kulawa da shi.
A cewar PRNigeria, wakilin kungiyar kare hakkin dan adam ta IHRC, ya ce an warware matsalar mahawara kuma El-Zakzaky ya ci gaba da karbar magani tare da Likitocin da aka fara bayarwa a gareshi.
7. Obasanjo Ya baiyana Abubuwa 3 Wadanda Zasu Inganta Najeriya
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gano da gabatar da wasu matakai ta musanman da zasu iya inganta da karfafar da Najeriya.
Tsohon shugaban kasar a mulkin soja da na dimokiradiyya ya bayyana a wata babban taron wake-waken kasa da cewa Yabo, Addu’o’i da Ibada ne zasu iya inganta da gina kasar. Ya kuma bayar da tabbacin hakan daga Littafi Mai Tsarki kamar yadda take a lokacin Yehoshafat,’ (II Labarbaru 20:22).
8. An gurfanar da Sojan Najeriya da laifin Fyade da Dalibar Jami’a
An gurfanar da Lance Corporal Sunday Awolola, jarumin soja da aka tsige daga tsaron kasa bisa zargin yiwa wata daliba mai digiri 300 a jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba Akoko, AAUA, Fyaden Dole a jihar Ondo.
Naija News ta gane da cewa an gurfanar da shi ne a ranar Laraba da ta wuce a Kotun Majistare da ke zaune a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com