Uncategorized
Wata Mata ta kashe Maigidanta a Jihar Kebbi don Kokarin komawa Saurayinta na da
0:00 / 0:00
Naija News Hausa ta karbi rahoton wata mata mai suna Auta Dogo Singe, wacce a yanzu haka tana hannun ‘yan sanda, da zargin kashe mijinta, Mista Abdulahi Shaho, don kokarin samun’ yancin komawa ga masoyiyarta, na da Idris Garba.
An bayyana a rahoton da cewa abin ya faru ne a cikin karamar hukumar Bagudo, Jihar Kebbi, inda Matar marigayin Singe, ta hada kai da Garba Hassan da kuma Sahabi Garba a nan kauyan Sabon Gari, yankin Bagodo, da bukatar kashe mijinta Abdullahi Shaho don koma ga Tsohon Masoyinta.
Naija News Hausa ta sami tabbacin zancen ne bisa bayanin Kwamishanan Jami’an tsaron Jihar, bayan wata zagaye da bincike da jami’an tsaro yankin suka yi.
Kwamishanan Jihar, Garba Muhammed Danjuma ya bayyana sunan tsohon masoyin matar a Idris Garba, wani mazaunnin garin Tugar Bature a karamar hukumar.
CP Garba ya kara ba da haske cewa hukuma ta riga ta kame Matar da kuma mutane biyun da suka hada hannu da ita don aiwatar da mugun al’amarin.
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.