Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 4 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 4 ga Watan Satunba, 2019

1. Xenophobia: Shugaba Buhari ya aika da Wakilai na musamman zuwa South Afirka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata da ta wuce ya aika da wakilai na musamman ga Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar South Afirka don tattaunawa kan harin ta’addancin da ake yiwa ‘yan Najeriya a kasar.

Wakilan kuma zasu isar da takaicin da bacin ran Shugaba Buhari game da kisan da ake wa ‘yan Najeriya da ke a kasar South Afirka.

2. Hare-Haren Xenophobic: Gwamnatin Najeriya Ta yi kira ga Babban Kwamishana a South Afirka

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci Babban Kwamishinan da ke wakilcin Najeriya a South Afirka, Bobby Moroe da ya dawo gida don bayyana yanayin da a ke ciki yayin da kashe-kashen ‘yan Najeriya ke ci gaba da karuwa a kullum.

Naija News ta samu labarin cewa Ministan Harkokin kasar Waje, Geoffrey Onyeama ya ba da wannan umarni bayan sabbin hare-hare ga ‘yan Najeriya da ke South Afirka.

3. Shugaba Buhari Ya Dakatar da Taron FEC

Naija News ta fahimci cewa Taron majalisar zartarwa na tarayya (FEC) ba zai gudana ba a yau Laraba, 4 ga watan Satumba.

An gane da cewa an soke taron FEC ne ta mako da mako da ake yi saboda cewa duk rubutattun tunatarwa da aka gabatar gaban majalisar don duba su an mayar da su ga Ma’aikatu daban-daban.

4. Mayaka ta Yankin Neja Delta sun gabatar da Barazanar ga Gwamnatin Shugaba Buhari

Kungiyar mai fafutukar yaki da kare yankin Neja Delta da aka fi sani da ‘Niger Delta Avengers (RNDA), watau kungiyar tsagera a yankin Neja Delta ta yi barazanar kawo kasar nan ga durkushewa ta hanyar lalata ayyuka da Sanfurorin mai da ke a yankin.

Kungiyar ta ce za ta aiwatar da barazanar ta idan Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da shirinta na daukar matakin kai Hukumar Gudanar da Cigaba ta Yankin Neja-Delta, (NDDC), daga Ma’aikatar Neja-Delta zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, OSGF.

5. Buhari ya Amince da karin Mukami ga Jami’an ‘Yan Sanda

A diban kokarin gudanarwa da kuzari a wajen aiki tuƙuru, Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya ya amince da karin girma da daukaka ta musamman ga jami’an ‘yan sanda.

Naija News ta fahimci cewa Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 3 ga Satumba a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

6. Sojojin Najeriya Sun Kama Mutane 4 da ke samar da kayaki ga ‘Yan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Talata da ta gabata, ta sanar da kama wasu masu samar da kayaki ga ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram a jihar Borno.

Naija News ta fahimci cewa Kwamandan gidan Tiyata ta Operation Lafiya Dole, Maj.-Gen. Olusegun Adeniyi ne ya sanar da hakan yayin da suka lalata motoci hudu da muhimman kayayyaki da aka kwace daga hannun maharan a cikin garin Maiduguri.

7. Shugaban kasar South Afirka, Ramaphosa ya fasa yin shuru game da harin ‘yan tawaye a kan’ yan Najeriya

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar South Afirka a ranar Talata, yayi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kaiwa ‘yan Najeriya da sauran baki a kasar.

Naija News ta fahimci cewa Ramaphosa ya aika da sakon Allah wadai a shafinsa na Twitter kan matakin da ‘yan kasar South Afirka suka dauka ta kisan ‘yan Najeriya.

8. Matsalar tsaro: Majalisar Dinkin Duniya ta aika da sako mai karfi ga Shugaba Buhari

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta magance matsalolin kashe-kashen da rashin tsaro da ke addabar kasar.

Madam Agnes Callamard, Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya na musamman game da rashin adalci, takaitawa ko aiwatar da hukuncin kisa, ta yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin da ta gabata.

Karanta kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com