Connect with us

Uncategorized

South Afrika ta Kulle Kamfanoninsu ta MTN da Shoprite da ke a Kano bayan an Haska Wuta a Ofishinsu

Published

on

An kulle Kamfanoni da mallakar kasar South Afirka wadanda suka hada da MTN da Shoprite, a cikin jihar Kano, ranar Laraba da ta gabata, bayan harin ramuwar gayya da ‘yan Najeriya a Kano suka kai wa kamfanonin bisa harin ‘yan Najeriya da kashinsu da ake yi a kasar South Afirka.

Naija News Hausa bisa rahotannai da manema labarai suka bayar, ta fahimta da cewa ofishin MTN da ke kan hanyar Civic, da ke tsakiyar birni Kano da kuma Shoprite a Ado Bayero Mall, kan Titin Zoo, na a kulle da mabuɗi.

A lokacin da aka tuntubi, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da cewa an riga an tura rukunin sojoji, jami’an tsaro da’ yan sanda dauke da makamai zuwa wuraren kasuwancin, don dakile duk wata zanga-zangar da ke afkuwa a wajajen.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa ba a Kano ne kawai aka kulle kamfanoni da Ofishin ba, harma da ta Ado, a Jihar Ekiti, da kuma Legas, bisa mayar da ramuwar gayya da ‘yan Najeriya ke kaiwa Kamfanonin da Mallakar kasar South Afrika da ke a Najeriya.