Labaran Najeriya
APC/PDP: Abinda Shugaba Buhari ya Fada bayan Nasara da Atiku a Kotu
Hukuncin Kotun Daukaka Karar Shugaban Kasa, Nasara ne Ga Yan Najeriya – inji Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce hukuncin da kotun daukaka karar shugaban kasa ta gabatar nasara ce ga ‘yan Najeriya da suka dage da tabbatar da zabensa a karo na biyu a karagar mulki.
Naija News ta ruwaito tun da farko cewa Kotun daukaka kara kan zaben Shugaban kasa (PEPT) a ranar Laraba ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP ta yi da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar suka gabatar a kotun.
Ko da shike Kotun daukaka karar shugaban kasar ta yi watsi da karar da Jam’iyyar All Progressive Congress Party ta yi wa Atiku Abubakar kan zargin cewa shi ba dan Najeriya ba ne.
Kotun daukaka kara ta Shugaban Kasa (PEPT) ta ce babu wata hujja da ta bayyana da cewa INEC ta fitar da sakamakon zaben shugaban kasa a kan layin yanar gizo.
A cikin hukuncin da aka gabatar a ranar Laraba, kotun ta ce masu karar – Atiku Abubakar da PDP, sun kasa shawo kan kotun kan cewa INEC ta samar da sakamakon zabe a kan layin yanar gizo.