Connect with us

Labaran Najeriya

Tunde Bakare Ya Bayar da Sabon Bayani game da Karbar Muki daga Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban Fasto da Janar Overseer ta Ikilisiyar Latter Rain Assembly, a jihar Legas, Fasto Tunde Bakare, ya ce faifan bidiyon da ya mamaye layin yanar gizo inda ya yi barazanar zama shugaban kasa, ya yi hakan ne kawai don bayyana burin sa.

Naija News ta tuno da cewa malamin ya shelanta a cikin wata Bidiyo da cewa zai karbi mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da wa’adinsa ya kare a shekarar 2023.

Bakare ya bayyana da cewa mutane ne suka tono bidiyon, da cewa lallai yayi fadi hakan amma tun da dadewa ne, kuma ya fadi hakan ne kawai ba da wata manufa ba amma dai don baiyana burinsa ga shugabancin kasar.

KARANTA WANNAN KUMA: Sanata Kwankwaso ya tallafawa daliban Kano 242 ga zuwa Karatu a Turai