Connect with us

Labaran Najeriya

Sabuwar Rahoto: Buhari ya Nada Mai shari’a, Tsoho A matsayin Alkalin Kotun Tarayya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Buhari Signing Minimum Wage Bill, Naija News Hausa, Hausa News, Labaran Hausa daga Naija News

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya mika sunan mai shari’a John Tosho ga Majalisar Dattawa don dubawa da tabbatar dashi a matsayin babban alkalin babbar kotun tarayyar kasar.

Naija News ta bayar da rahoton ne da tabbacin cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aika wa majalisar dattijan Najeriya wanda shugaban majalisar zartarwar kasar, Ahmad Lawan ya karanta a ranar Talata (yau), 29 ga Oktoba 2019.

Game da nadin alkalin babbar Kotun Tarayyar, Shugaba Buhari ya ce:

“Saboda bin sashi doka na 250 (1) na kundin tsarin mulkin tarayyar kasar Najeriya na tun 1999 (kamar yadda aka yi gyara), a haka na wallafa don neman tabbatarwar Majalisar Dattawa ga nadin Mai Shari’a Mai Girma JT Tsoho a matsayin Babban Alkalin Babbar Kotun Tarayyar Najeriya.

“Duk da shike na yi imanin cewa Majalisar Dattawa za ta duba wannan bukatar ta hanyar da ta saba, don Allah, Sanatan Shugaban Majalisar Dattawa, a karba a kuma tabbatar da girmamawa sosai” in ji Buhari.

KARANTA WANNAN KUMA; An Kashe Baghdadi, Shugaban Kungiyar ISIS.