Labaran Najeriya
Tsohon Ministan Sufuri, Kayode Ya Kalubalanci Ahmed Lawan kan Zancen Shugaba Buhari
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama a karkashin Gwamnatin Goodluck Jonathan, Femi Fani-Kayode, ya bayyana majalisar dattawan Najeriya a jagorancin Ahmed Lawan a matsayin taron tawul.
Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman Shugaban Majalisar Dattawar cewa duk wata bukata daga Shugaba Muhammadu Buhari abu ne mai kyau ga kasar Najeriya.
Naija News Hausa ta fahimci cewa Lawan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar girmamawa da Itse Sagay ya kai a ofishin sa ranar Alhamis.
Bayanin Lawan na kamar haka;
“Ina so in tabbatar muku cewa duk wata bukata da ta fito daga hannun Shugaban kasa bukata ce da za ta sanya Najeriya ta zama kasa mafi dacewa dangane da alƙawura ko kuma majalisar, Majalisar dattijai kuwa za ta yi aiki da sauri don tabbatar da cewa mun taka tamu rawar don tabbatar ko kuma ƙaddamar da dokokin, yadda yakamata.”
A shirye muke, a zahiri, zamu hanzarta kuwa idan wadanan takardar suka isa a teburinmu, a shirye muke don mu fara aiki akan su,” in ji shi.
Wannan ne Fani-Kayode ya mayar da martani akai a layin yanar gizon sa ta Twitter.
Ya rubuta cewa, “Duk wani bukata daga Buhari yana da kyau ga kasar. Za mu yi aiki a kansa – Shugaban Majalisar Dattawa Shuaibu Lawan.”
“Ku yi la’akari da abubuwan da Shugaban Majalisar Dattawa ya fada. Majalisar kasa an sanya ta ne a matsayin rukunin da zata yi tantancewa da kuma daidaitawa ga ikon zartarwa, amma ba kamar tambarin roba ba!” inji Kayode.