Labaran Najeriya
Kada Ku Bawa Buhari Rancen Kudi – Inji Cif Olabode
Cif Olabode George, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya yi kira ga kasashen waje da kar su bai wa Shugaba Muhammadu Buhari rancen kudi da yake bukata.
Mista George ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani game da shirin rancen dala biliiyan $29.96 na 2016-2018 da Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa saboda dubawa da amincewarsa.
“kasashen turai za su yi dariya da ba’a ga Najeriya saboda karbar irin wadanan bashi, saboda ya koka da yadda ake asarar kudaden kasar ta hanyar gudanar da yauka.
Da yake zartawa da manema labaran kamfanin dilancin labarai ta Daily Independent, George ya ce: “Shugaba Buhari yana neman ya je ya kara cin bashi a yanzu. Zasu tambayeshi ”Shin ka duba abubuwan da ke faruwa a kasarka”. Me zai sa mu baku bashin kudi? Bai dace su bashi komai ba.”
“Shin kasashe nawa na Afirka kuke gani da neman rance da irin waɗannan abubuwa? Duk waɗannan tallace-tallacen da ba a buƙata da ake yadawa a kan CNN daga kamfanonin Najeriya kan samfuran da suke na Najeriya zancen banzaa ne.”
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya ya bayyana da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya halarci bikin bude makarantar jami’ar sufuri a Daura.
Ka tuna cewa Daura a jihar Katsina ita ce garin shugaba Buhari.
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shugaban ya isa Daura ne da yammacin ranar Juma’a, a bayan ya halarci taron kolin kungiyar kasashen waje na fitar da Gas a Malabo, a karkarar Guinea.