Uncategorized
Dino: Majalisar Dattawa Ta Rantsar da Smart Adeyemi a Matsayin Sanata A Jihar Kogi

Naija News ta tuno da cewa Adeyemi ne yayi nasara da lashe zaben fidda gwani da aka gudanar kwanan nan a gundumar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar a Jihar Kogi.
Smart ya lashe zaben ne da kayar da babban abokin adawarsa a takarar, Sanata Dino Melaye, dan takara daga Jam’iyyar PDP.
A lokacin rantsar da Adeyemi, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yanzu tana da Sanatoci 63 a cikin Babban majalisa, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuwa na da sanatoci 46 hadi da Young Democratic Party (PDP) da memba guda daya tak.