Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Amince Da Nadin Sakatarorin Dindindin Tara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sakatarorin tara a cikin Ma’aikatan Farar hula na tarayya.

A wata sanarwa wacce ke dauke da sa hannun Daraktan Sadarwa, Ofishin Shugaban Ma’aikata na Rundunar, Olawunmi Ogunmosunle, mukaddashin shugaban hukumar farar hula, Dokta FolasadeYemi-Esan, ya ce za a sanar nan jim kadan da lokacin rantsar da su da kuma sanya mukamai.

Sabbin sakatarorin dindindin sun hada da; Musa Hassan daga jihar Borno; Ahmed Aliyu daga jihar Neja; Olushola Idowu daga jihar Ogun; Andrew Adejoh mai wakiltar yankin Arewa ta Tsakiya; Umar Tijjani mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas; Nasir Gwarzo daga yankin Arewa maso Yamma; Nebeolisa Anako mai wakiltar yankin Kudu maso Gabas; Fashedemi Peter mai wakiltar yankin Kudu maso Yamma; da Evelyn Ngige daga yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

An zabi sabbin sakatarorin dindindin ne daga daraktoci 48 da suka halarci hirar bakin da aka gudanar a makon da ya gabata.

Manyan jami’an 48 sun fito da nasara ne a cikin ‘yan takarar 87 da suka tsaya wa jarabawar na kashi biyu na masu neman aikin, wanda aka gudanar a makon da ya gabata.