Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Bar Najeriya Zuwa Kasar Masar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata, 10 ga Disamba, 2019, ya bar Najeriya zuwa Aswan, kasar Egypt, don halartar taron Aswan.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an tsara dandalin ne don kawo Cigaba ga Afirka.

Taron wanda zai fara gudana daga ranar 11 zuwa 12 ga Disamba, 2019, wani shiri ne na magance dangantakar dake tsakanin zaman lafiya da ci gaba a Afirka yayin inganta hanyoyin da ake bi a kasashen Afirka ta hanyar karfafa manufofi da ayyuka.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ne ya gabatar da wannan kudurin a matsayinsa na Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Ana sa ran taron zai hada shugabannin jihohi da gwamnatoci, shugabanni daga kungiyoyi na yanki da na kasa da kasa, cibiyoyin hada-hadar kudi, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula gami da masana, da kuma manyan masana don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi barazana, kalubale da kuma zarafi.

Gwamnonin Najeriya da suka bi Shugaba Muhammadu Buhari zuwan taron sun hada da Ahmadu Fintiri na Adamawa, Godwin Obaseki na Edo da Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Sauran sune: Ministan Tsaro, Gen. Bashir Magashi (Rtd); Ministan Jiha, Harkokin Waje, Amb. Zubairu Dada; Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (Rtd); da Darakta Janar, Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

Naija News Hausa ta tattara da cewa Shugaba Buhari zai dawo kasar Najeriya ne ranar Juma’a bayan karshe taron.