Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Reshen Jihar Katsina sun Kame Wani Shugaban ‘Yan Fashi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta kama wani mugun shugaban ‘yan fashi da garkuwa, mai shekaru 20 ga haifuwa da suna, Aliyu Sani na Sabuwar-Unguwa barikin soja, Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani taron manema labarai ta ranar Litinin a Katsina.

Ya bayyana da cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 4 ga wata Disamba, a cikin garin Katsina, bayan wata likin sirri da suka karba.

“Wani lokaci cikin watan Afrilu, wanda ake tuhumar ya hada kai da Abdulrahman Danfillo, mai shekara 25, adireshi iri daya, wanda yanzu haka aka yaudari da kuma sace wani mai suna Abubakar Muhammad da Aliyu Ahmed, dukkansu mazauna Sabuwar-Unguwa, Katsina.”

“Wadanda ake zargin sun dauki wadanda suka sace din zuwa ga wasu ‘yan fashi a dajin Gora da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.”

“An tilasta Mahaifin Abubakar Muhammad da biyan Naira dubu dari da hamsin N150,000 a matsayin kudin belin dan sa, yayin da Aliyu Ahmed ya samu tserewa daga kogon ‘yan fashinr.” Inji shi.