Connect with us

Uncategorized

Tirela Ta Rutsa Da Wata Motar Kasuwa a Nyanya, Abuja, Sanadiyar Mutuwar Wata Mata

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A wani rahoto da jaridar Punch Metro ta bayar a yau, wadda wakilin mu ta Naija News Hausa ya gano, ta ce wata mace ta mutu bayan da babbar motar tirela da ke dauke da tirakto a cikinta ta fada wa motar da suke a ciki.

Tirelan ya fada ne kan motar kasuwa, wace ake kira Taxi a nan shiyar Nyanya, Abuja.

Lamarin wanda ya faru da misallin karfe 9.40 na safiyar yau, Laraba, ya kai ne ga faduwar motar da ke dauke da lambar rajista KSB379XA (Kwara), inda ta rutsa kan wata motar manema labaran jaridar Punch Metro, kamin motar ta tsaya a tashar bas ta Nyanya.

Wani wakilin jaridar Punch Metro, wanda ke cikin motar sa a lokacin hadarin, ya tsira ba tare da wani rauni a jikinsa ba.

Marigayiyar, wata tsohuwa ce mai ‘yan shekaru, tana zaune ne a kujerar fasinja ta motar wacce ta mutu a nan take a yayin da hadarin ya faru.

Shi kuma direban motar a haka an riga an kai shi asibiti don bashi kulawa ta musanman.

Rahoto ta nuna da cewa motar ta rasa birkunanta ne a yayin kan tafiya a kan hanyar barikin soja na Mogadishu, wanda ke bakin Babban Birnin Tarayya, kilomita da yawa kafin ta tsaya.

An ce direban babban motar ya yi ari na zomo ne da sheqawa a yayin da hadrin ya faru, ya kuwa yi watsi da babbar motar.

A haka Jami’an Hukumar Kula da Tafiye-tafiyen motoci hadi da ‘yan sanda sun isa wurin.

Idan an samu karin bayani, zamu sanar a shafin labarai jim kadan da nan.

KARANTA WANNAN KUMA; Ba Zan Sake Neman Matsayi Ba a Zaben Najeriya – Inji Danjuma Goje