Labaran siyasa
Labaran Karya Ne Ake Yadawa, IBB Bai Mutu Ba – Kassim
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Ibrahim Badamosi Babangida (IBB), tsohon Shugaban Najeriya bai mutu ba, kamar yadda ake yada wa a wasu kafafen labarai.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa rahotanni sun bayyana a wasu sassan kafafen yada labarai na Najeriya a safiyar ranar Lahadi, inda suke nuni da cewa Tsohon Shugaban na Najeriya ya mutu amma mai magana da yawun sa ya fitar da sanarwa inda ya karyata rahoton.
Mai magana da yawun IBB, Kassim Afegbua a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, 15 ga Disamba, ya bayyana rahotannin mutuwar IBB da cewa “labarai ne na karya”.
Afegbua a cikin sanarwan ya ce:
“Labari ne na karya wanda aka saba yadawa da tsawon lokatai a yanzu da fatan namu IBB, wanda muke sawa shi a zaman “Babban Jarumi na Karshe a Kasa” a fagen siyasar Najeriya, ya mutu.
“Kudurin Hukunci Kan Dokar Labaran Karya” zai tamaka da magance irin wannan labaran karyar. IBB yana da rai da kuma koshin lafiya. A yanzu haka ya fara ganawa da abokan arziki da ta siyasa a yau, Lahadi, 15 ga Disamba 2019 a nan gidan sa na tsaunin Minna. Yana cike da rayuwa kuma a yanayin halayyar sa.”
“Ya Allah ka gafartawa wadanda suke son IBB ya mutu. Allah ne mai bayar da ɗaukar rai, ba mutane ba. Mutuwa, azaman rigar kowane halitta tabbas zai zo ga kowa da rana ko kuma lokacin da aka tsara da sa’a, amma da gangan ana yada labaran karya da begen wani ya mutu, wannan mumunar yanayi ne.
Allah Ya gafarta masu. IBB, da alherin Allah masani da kuma mai iko duka, zai rayu don cikar da tafiyarsa da makomar rayuwarsa, har a ganin wadanda suke masa fatan mutuwa. Wannan shine kusan karo na uku a wannan shekara da ake yada wannan zancen karyar.” inji Shi.