Connect with us

Labaran Najeriya

Ban Gamsu Da Tsarin Dimokradiyya Ba – inji Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai gamsu da tsarin dimokuradiyya ba, musanman yanayin tafiyar hawainiya ta tsarin ba.

Wannan itace zancen shugaba Buhari bisa yadda aka samar a kan labaran yanar gizo da Gistmania ta bayar, cewa shugaban ya fadi haka ne yayin da yake wata hira da gidan talabijin na kasa, NTA yayin murnan cika sheakaru 77.

Buhari wanda ya kwatanta mulkinsa a matsayin soja da na tsarin demokradiyya ya ce “Lokacin da na yi shugabanci a mulkin Soja, na tattara wadanda ke jagoranci, na dauke su zuwa Kirikiri (Kurkukun Tsaro Mafi Girma) na fada masu cewa su masu laifi ne, kuma sai sun tabbatar da cewa su ba masu laifi ba ne kamin a sake su,”

Buhari ya ce, “yayi ​​koyi ne a cikin mawuyacin yanayi,” amma cewa ba zai iya yin hakan ba a tsarin dimokiradiyya.

“Na kafa tsaro ga kusan dukkanin kwamitocin yankuna don binciken su. Wadanda aka gano suna rayuwa fiye da yadda hanyan samun kudin su, na kuwa sa an amshe mallakarsu da ba da shi ga jihohi.”

“Amma ni da kaina an kama ni daga baya, aka tsare ni kuma aka ba su abin da suka sata

“Amma a karkashin wannan tsarin da ake ganin ya fi cancanta da lissafi, tsarin ya fai sanyi kamar tafiyar hawainiya a gareni, amma dole in bi tsarin,” in ji shugaba Buhari.