Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Kano Ya Haramta Daukar Macce Da Namiji Cikin Keke Napep Daya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa shigar namiji da macce a cikin ‘Keke Napep’ guda a fadin jihar daga watan Janairu, 2020.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a bikin rufe taron shekara da shekara karo na 77 da kungiyar shirya hutu ta Musulunci (IVC) wanda Zone A na kungiyar ‘Muslim Society of Nigeria (MSSN)’ ta gudanar a Jami’ar Bayero, Kano.

Naija News Hausa ta fahimci cewa a taron wanda Kwamandan Hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya wakilci Gwamna Ganduje, ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar kiyaye martabar addinin Musulunci ne.

Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ne ya fara gabatar da tsarin ‘Keke Napep’ wanda aka fi sani da ‘A Daidaita Sahu’ don daukan mata kawai a Kano tun farko a lokacin da yake shugabancin jihar.

Wannan ya biyo ne bayan da gwamnatin Shekarau ta haramtawa ‘yan kabukabu da daukar mata.

Amma tun bayan ficewar tsohon gwamna, Shekarau,  an bayar da damar ci gaba da daukar mutane daga dukkan jinsi, watau macce da namiji a shiga guda, wanda a haka gwamnatin jihar ta yi yunkurin canza yanayin.

A wajen hidimar, Gwamna Ganduje ya kuma gargadi mahalarta da su fuskanci karatun su da kuma kaurace wa shan kwayoyi.