Shugaba Muhammadu Buhari Na Ganawar Siiri Da Shugabannan Hukumomi | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Shugaba Muhammadu Buhari Na Ganawar Siiri Da Shugabannan Hukumomi

Published

Naija News Hausa ta fahimta a yau Litinin da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawar siiri da tare da wasu shugabannin hukumomi a nan Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Ko da shike ba a bada hasken dalilin taron ba, amma ana sa ran shugabannan za su tattauna ne kan sake duba yanayin tsaro a kasar da wasu zance kuma da ta shafi ci gaba.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa an yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yarda ‘yan ta’adda su raba kasar biyu ta hanyar addini.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu da kuma aka bayar ga manema labarai bayan wata kisa da ‘yan kungiyar ISWAP suka yi na kashe Kiristoci goam sha daya a ranar kirsimeti.

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].