Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 31 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 31 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari ya Tsauta Wa Ministoci Da Mataimakansu da Tafiye-tafiye

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da wasu sabbin umarni da ke takaita adadin lokuta da Ministoci zasu iya tafiya a cikin shekara guda.

Ministan yada labarai, al’adu da yawon shakatawa, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.

2. Buhari Da Bakare Sunyi Wani Ganawar Siiri A Aso Rock

Fasto Tunde Bakare, babban Fasto na Majami’ar Latter Rain a ranar Litinin, ya yi wata ganawar siiri da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a Aso Rock Villa, Abuja.

Ganawar siiri da Bakare yayi tare da Shugaban kasar ta fara ne da misalin karfe 3 na rana, kuma ya dauki kusan mintuna 30 kamin karsheta a fahimtar Naija News.

3. Buratai Ya Kaurace Wa Taron Da Buhari Yayi Da Shugabannin Ma’aikata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ya yi wata ganawar siiri da shuwagabannin ma’aikata a gidan gwamnati da ke Abuja, an yi imanin cewa taron itace na karshe ga shekara ta 2019.

An yi imanin cewa taron ya kasance ne kan zancen tsaron kasa daga hannun shugabannin tsaro.

4. Buba Galadima Ya Bayyana Wanda Shugaba Buhari yake Tsoro Fiye Da Allah

Buba Galadima, wanda shine tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tsoron ‘yan farar fata, musamman gwamnatin Amurka fiye da Allah.

Naija News ta ruwaito cewa Galadima yayi wannan furucin ne yayin martani kan ikirarin da Lauyan Janar din kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayar cewa an saki Sambo Dasuki, tsohon mai ba da shawara kan harkar tsaro, da Omoyele Sowore, dan jaridar Sahara Reporters, bisa dalilan jin kai.

5. 2023: Buba Galadima ya aika da Gargadi mai karfi ga Tinubu game da Buhari

Alhaji Buba Galadima, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma tsohon abokin hamayya na Shugaba Muhammadu Buhari, ya koka da cewa shugaban kasar ba ya taba taimaka wa kowa.

A cikin bayanin Galadima, ya kara da cewa ba a san Buhari da taba taimakawa wadanda suka taimaka masa a harkan siyasa ba.

6. Gwamnatin Legas Tayi Ikirarin Kame Duk Asibitocin Da Suka gaza bada Kulawa ga wadanda suka jikkata da harbin bindiga

Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga dukkanin asibitoci da wadanda ke a fannin kiwon lafiya, hadi da wadanda ke cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da na masu zaman kansu da ke aiki a jihar da su daina yin watsi da wadanda ‘yan bindiga suka rutsa da su.

Gwamnatin jihar ta kuma nemi asibitocin da su janye daga halin guji da rashin bada kulawa ga masu mugun rauni a kan uzurin neman rahoton ‘yan sanda ko kuma bukatar samar da shaidar kudade kafin fara jinyarsu.

7. 2020: ‘Yan Najeriyar Za Su Fuskanci Mawuyacin Yanayi A Karkashin Mulkin Buhari – Shehu

Shehu Sani, tsohon Sanata wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a jagorancin Sanatoci na 8 na Najeriya, ya ce ‘yan Najeriya za su kara fuskantar wahala a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2020.

Naija News ta samu labarin cewa tsohon dan majalisar ya yi wannan tsokaci ne yayin wani shirin rediyo a gidan Rediyon Invicta FM a Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.

8. PDP Ta Kalubalanci APC Akan Yawan Karuwar Rashin Aiki A Najeriya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sake yin tir da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan karuwar rashin aikin yi a kasar.

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, ya fada da cewa jam’iyyar APC cewa ta lallatar da harkokin kasar ta hanyar tafiyar da harkokin a siyasance da musanman kan yanayin rashin aiki a kasar, da kuma cewa su shirya don fuskantar kalubalan ayukansu a shekara ta 2023.

Ku sami kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a shafin Naija News Hausa