Connect with us

Uncategorized

Wuta ta barke a Kasuwar Mariri, Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan awowi kadan da shiga watan Fabrairun, mun samu tabbacin wata hadarin wuta da ya kame shaguna a kasuwa Mariri da ke a Jihar Kano a nan yankin Dawakin.

Abin ya abku ne a ranar Alhamis da ta gabata, Kasuwar Mariri (‘Yan Itace) a nan yankin Dawakin ta Jihar Kano, kamar yadda muka samu labarin hakan a Naija News Hausa ta bayanin Alhaji Saidu Mohammed, kakakin yada yawun Hukumar Kashe kamun Wuta (Fire Service) na Jihar.

Alhaji Saidu ya ce “Mun samu kiran gaggawa ne daga wani mazaunin wajen mai suna Ismail Mohammed da cewa kasuwar ta kama da wuta”

“Ismail ya kira hukumar ta mu ne da safiyar ranar Alhamis da cewa shaguna Ukku sun kame da wuta a cikin kasuwar a misalin karfe 2:38 na asuba’i. Daga jin hakan sai muka yi wuf da motar kashe wutar mu da wasu ma’aikata kadan muka hari wajen”

“Mun samu isa kasuwar ne misalin karfe 2:45 na safiya don kashe wutar bisa kirar da Ismail yayi mana” in ji Alhaji Saidu.

Alhaji Saidu ya shawarci ‘yan kasuwa da daina amfani da kayaki ko kuma abubuwan da zai iya kyasta wuta a cikin kasuwar.

Ya bayyana da cewa bayan kamuwar wutan da ya faru a kasuwa, sun sami wata kira kuma da cewa dakuna biyu sun kame da wuta a wata anguwa da ake kira Sabon Gari a hanyar Onitsha, misalin karfe 10:35 na safiya, bayan waccan kamun wutar na kasuwar Mariri, a nan yankin.

“Dakuna biyu sun ci da kamun wutar kamin isarmu a wajen” inji shi.

“Ku daina amfani da kayakin da za su iya kyasta wuta da kansu a cikin kasuwa da kuma gidaje, ku rika ajiyar bokitin kashe wuta da kuma kayakin da za a iya kashe wuta da shi idan irin hakan ya faru kamin isowar mu” inji Alhaji Mohammed.

Karanta wannan kuma: Rikici ta barke tsakanin ‘yan shirin Fim na Hausa