Labaran Najeriya
Ku zabi Buhari don samar da ayuka a kasa – Farfesa Osibanjo
Farfesa Yemi Osibanjo, mataimakin shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan Najeriya da su zabi Buhari don samar da ayuka da yawa ga masu neman aiki.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai samar da aiki da daman idan har an sake zaben sa ga shugabancin kasar” inji Osibanjo.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Osinbajo yayi hadarin jirgin sama ranar Asabar da ta gabata a yayin da yake kan hanyar zuwa Jihar Kogi don gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa.
Mun sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnan sa da irin mataimaki da yake da shi.
“Ina murna matuka yadda Allah ya kiyaye Osibanjo a hadarin jirgin saman, kuma abin yabawa, bai fasa ga tafiyar da hidimar yakin neman zaben ba bayan hadarin”
“Na jinjina ma Osibanjo da irin sadaukarwa da halin mazantaka, Allah ya kara masa lafiyar jiki da kuzari na taimakawa kasar Najeriya” in ji Buhari.
Mun samu rahoto a Naija News da cewa Osibanjo ya bayyana a karamar hukumar Nsit ta Jihar Akwa Ibom a lokacin da ya je don yawon hidimar neman zabe da cewa “Buhari zai samar da ayuka da daman idan har aka sake zaben sa a matsayin shugaban kasa a Najeriya”.
Ya kara da cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar da ayuka 500,000 ga matasa ta hanyar NPOWER.
“Buhari na kokarin ganin cewa ba aiki kawai zaku samu ba, amma aiki mafi kyan gaske”
“Gwamnatin Tarayya na shirin kaddamar da wata shirin wadda banki zata bayar da tallafin kudi ga Matasa da ‘Yan Mata don taimakawa tattalin arzikin kasa ta hanyar hidimar N-Power” inji Osibanjo.
Ya shawarci Jama’ar Jihar da cewa su zabi Jam’iyyar APC, su kuma zabi shugaba Muhammadu Buhari don samar da ci gaba a kasar Najeriya.
Karanta wannan kuma: