Uncategorized
An kai ga karshen Yajin Aikin ASUU
A ranar jiya Alhamis, 7 ga watan Fabrairun, 2019, Hukumar Mallaman Jami’o’i da Gwamnatin Tarayya sun kai ga arjejeniya akan dakatar da yajin aikin da Hukumar ASUU ta soma watannai Ukku da ta gabata a kasar.
Hukumar ASUU ta dakatar da yakin aikin ne bayan ganawar awowi biyu da ta yi da gwamnation tarayya a birnin Abuja.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Mallam Adamu Adamu, Ministan Ilimi ya yi kira ga mallaman makarantan jami’o’i duka da cewa su yi hakuri da gwamnatin tarayya akan wannan yajin aikin. Ya fadi wannan ne a makarantar jami’ar Federal Polytechnic Offa, da ke nan Jihar Kwara a ranar Alhamis 17, ga watan Janairu, 2019.
Ya ce “An kusa a kawo yajin aikin ga karshe”.
“An kaddamar da dukan alkawalai da arjejeniya takwas 8, da ke tsakanin hukumar ASUU da gwamnatin tarayya. An kuma soma fara aiki akan wadansu daga cikin arjejeniyar” inji bayanin Chris Ngige, Ministan Aikace-aikace kasa, kamar yadda ya bayar ga manema labarai a ranar Alhamis da ta wuce a birnin Abuja.
Ngige ya kara da cewa Gwamnati ta bayar da kudi naira biliyan N25b don sabanta wasu ayuka da ya shafi jami’o’in kasar tsakanin Watan Afrilu da watan Mayu, a shekara ta 2019. Daga baya kuma sai a kadamar da ayukan shekarar 2009 kamar yadda aka ajiye a shekarun baya, inji shi Ngige.
A ganin kai ga wadannan arjejeniyar, shugaban hukumar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bada umurni ga shugabannan hukumar da Jami’o’i da dakatar da yajin aikin daga ranar jumma’a, 8 ga watan Fabrairun, shekarar 2019.
Duk da kai ga arjejeniyar, Ogunyemi ya ce “Zamu iya komawa ga yajin aikin a kowace lokaci idan har gwamnatin tarayya bata cika sauran alkawalan su ba ga hukumar” inji shi Farfesa Biodun.