Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 22 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 22 ga Watan Fabrairun, 2019

1. Shugaba Buhari yayi gabatarwa ga jama’ar Najeriya akan layi

A yau Jumma’a, shugaba Muhammadu Buhari yayi gabatarwa ga jama da cewa su fito don jefa kuri’ar su a ranar Asabar ga zaben shugaban kasa da ta gidan Majalisa.

Shugaban ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatarwa akan zaben kasar Najeriya ta shekaran 2019, musanman zaben shugaban kasa da za a fara a ranar Asabar ta gobe.

2. Kotu ta bayar da dama ga Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara don tseren zaben shekarar 2019

Muna da sani a baya da cewa Kotun kara ta birnin tarayya ta dakatar da Jam’iyyar ga daman tseren zaben shekarar 2019.

Kotun ta sake bayar da dama ga jam’iyyar don smaun daman takaran ga tseren zaben.

3. ‘Yan ta’adda sun hari Sanata Rabiu Kwankwaso har sun kashe mutane da kone motoci

Mahara da bindiga sun kai wa tsohon gwamnar Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a kauyan Kofa ta karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano.

Mun gane a Naija News da cewa ‘yan harin sun kone a kila motoci 10 kumurs da wuta a wajen harin.

4. ‘Yan takaran shugaban kasa 12 suka janye daga tseren takaran don marawa shugaba Buhari baya

Kimanin ‘yan takaran shugaban kasa goma sha biyu (12) suka janye daga tseren takaran shugaban kasa don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya ga cin nasaran kujeran shugaban kasa.

‘yan takaran sun gabatar da janyewar su ne da kuma marawa shugaba Buhari baya a ranar Alhamis da ta gabata a birnin tarayya, Abuja.

5. Shugaba Buhari zai gabatar da murnan sa ga duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa – inji Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC sun bayyana da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai yi gaisuwar murna ga duk wanda ya lashe tseren takaran shugaban kasar Najeriya ga zaben 2019.

“Kuma shugaban zai godewa jama’ar Najeriya da irin goyon bayan su ga fitowa don jefa kuri’un su a matsayin ‘yan kasa” inji rukunin takaran shugaba Buhari.

6. Ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe ya janye zuwa Jam’iyyar APC

‘yan awowi kadan ga zaben shugaban kasa da ta gidan majalisar dattijai, Ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar yobe ya gabatar da janyewar sa daga jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC don goyan bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Dan siyasan, Alhaji Sani Inuwa Nguru, ciyaman na jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, ya bayyana janyewar sa daga Jam’iyyar a birnin tarayya, Abuja don goyon bayan Buhari da Jam’iyyar APC ga zaben 2019.
Yayi wannan gabatarwa ne a ranar Alhamis da ta gabata.

7. Ba zan janye daga matsayina na shugaban hukumar INEC ba – Mahmood Yakubu

Shugaban hukumar gudanar da zaben kasa,Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana da cewa ba zai janye daga kujerar sa na shugaban hukumar ba bayan zaben 2019.

“Ban ga dalilin da zai sa inyi hakan ba” inji shi.

Mahmood ya bayyana hakan ne don mayar da martani game da zancen da ake na cewa watakila yana da muradin janye wa daga kujerar sa bayan zaben 2019.

8. Hukumar EFCC sun daga murya akan kudin dala mara kyau da ya mamaye kasar Najeriya

Hukumar kula da hukunci akan Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) sun gane da cewa kudin dala mara kyau ya mamaye kasar Najeriya a wannan lokaci, musanman ga zaben ranar Asabar da za a fara a kasar Najeriya.

Hukumar sun gabatar ne da hakan a wata sanarwa da aka sanya hannu daga wajen shugaban hukumar, Ibrahim Magu, da cewa sun kula da cewa kudin ya mamaye ko ta ina a kasar.

9. Aisha Yesufu ta gabatar da dalilin da yasa ta janye ga goyon bayan shugaba Buhari

Matar da ta gabatar da hidimar ‘BringBackOurGirls’ lokacin da aka sace ‘yan makaranta Dapchi, Aisha Yesufu, ta bayyana dalilin ta na janyewa daga goyon bayan shugaba Buhari.

“a shekara ta 2015, na bayar da goyon baya na kashi 100% ga shugaba Muhammadu Buhari ga zabe, amma a shekarar 2016 sai na janye daga goyon bayan shugaban da na kula da irin rashin nuna kulawa ta musanman da shugaban yayi da iyalan yaran da aka sace a lokacin” inji Aisha.

10. Ban janye ba daga matsayina na mataimakin shugaban kasa – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya fada da cewa bai janye ba daga matsayin sa na mataimakin shugaba Buhari ga shugabancin kasar Najeriya.

Farfesa Yemi ya bayyana hakan ne a yanar gizon nishadarwa ta twitter don mayar da martani ga zancen da ake yi gareshi na janye wa daga matsayin sa na mataimakin shugaban kasa.

Ka sami cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa.